Gwamna Radda Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 3, Ya Ja Masu Kunne gaban Jama'a
- Gwamna Dikko Radda ya rantsar da sababbin kwamishinoni uku da manyan sakatarori takwas a gidan gwamnatin Katsina
- Radda ya yaba da jajircewar sababbin mukarraban gwamnatin, musamman Yusuf Jibia, Aisha Aminu, da Injiniya Sirajo Abukur
- Gwamnan ya ce nadin sababbin sakatarori wani bangare ne na gyaran ma’aikatu da inganta aikin gwamnati ga al'ummar Katsina
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rantsar sababbin kwamishinoni uku da manyan sakatarori takwas.
A yayin da yake rantsar da su, Gwamna Radda ya ja hankalin kwamishinoni da sakatarorin da su dauki mukaman a matsayin amanar al’umma.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya nada sababbin kwamishinoni
Taron da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Katsina, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ciyamomi da iyalan wadanda aka nada, inji rahoton TVC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dikko Radda ya bayyana wannan mataki a matsayin wani sabon salo na inganta gaskiya, amana, da samar da ingantaccen shugabanci.
Gwamnan ya ce wannan nadin na zuwa ne yayin da gwamnatinsa ke nazarin ayyukan da ta gudanar cikin shekara biyu da rabi, domin karfafa tsarin gudanarwa.
“Mun yi shekaru biyu da rabi a mulki, lokaci ne na duba irin ayyukan da muka gudanar, da sake daura damarar wasu karin ayyukan,” in ji Gwamna Radda.
Matsayin sababbin kwamishinoni ga Radda
Ya yaba da kwarewa da amanar sababbin kwamishinonin, musamman Hon. Yusuf Suleiman Jibia, wanda ya bayyana a matsayin “ɗan siyasa mafi gogewa a majalisar zartarwa.”
Radda ya kuma yabi Hajiya Aisha Aminu, wadda ta yi fice wajen inganta harkar matasa da mata a fannin kasuwanci lokacin da take jagorantar KASEDA.
“Na zabi yin aiki da ita ne saboda jajircewarta da kuma bukatata na kara wakilci ga mata a gwamnati."
- Gwamna Radda.

Kara karanta wannan
Suswam: Tsohon gwamna ya musanta satar dukiyar jama'a, ya fadi inda ya samu kudinsa
Gwamnan ya bayyana Injiniya Sirajo Yusuf Abukur a matsayin alamar karfin matasa a gwamnati, yana mai yabawa da irin gudunmawar da ya bayar a KASROMA wajen gina hanyoyi.
Ya ce nadin Sirajo ya nuna adalci da wakilci ga karamar hukumar Rimi, wadda ba ta taba samar da kwamishina tun bayan komawar mulki ga farar hula ba, in ji rahoton Channels TV.

Source: Facebook
Gwamna ya rantsar da sababbin sakatarori 8
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa nadin sababbin manyan sakatarori wani bangare ne na kokarin gwamnati wajen gyaran ma’aikatu da inganta aikin gwamnati.
“Muna sa ran za ku kasance ginshikai wajen tabbatar da tsari, kwarewa, da aiki mai inganci,” in ji Dikko Radda.
Wadanda aka rantsar sun hada da: Yusuf Ahmed (Katsina), Aminu Ibrahim (Katsina), Aishatu Abdullahi (Dutsinma), Dasuki Ibrahim Abubakar (Malumfashi), Lawal Abashe (Matazu), Ado Yahaya (Sabuwa), Sani Rabi’u Jibiya (Jibiya), da Nasiru Ladan (Kaita).
Radda ya rantsar da kwamishinoni 20
Tun da fari, a 2023, Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Dikko Radda ya rantsar da sababbin kwamishinoni 20 da kuma mashawarta 18.
A jawabin da ya yi a wurin bikin rantsarwan, Radda ya ce galibin sababbin kwamishinonin mutanen mazaɓarsu ne suka zaɓe su bisa cancanta da kuma amana.
Raɗɗa ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu da kwazo da jajircewa maimakon su riƙa binsa duk inda ya je domin gudanar da aikinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

