Gwamna Ya Kakaba Haraji kan Masu Jana'za, Aure da Suna ? An Ji Gaskiyar Lamari
- Gwamnatin Oyo ta yi karin haske kan jita-jitar da ke cewa za ta kakaba haraji a bukukuwan aure, suna da jana’iza
- Gwamna Seyi Makinde ya ce rahoton da ake yadawa ba gaskiya ba ne, kuma ya zargi wasu da neman tayar da hankula
- Ya yi gargadin cewa yayin da zaɓe ke gabatowa, wasu ‘yan siyasa za su ƙirƙiri labarai don bata suna gwamnatinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta yi martani mai zafi ga wasu da ke yada karairayi domin tayar da hankulan al'ummar jihar domin biyan buƙatar kansu.
Gwamnatin ta yi magana ne kan yada jita-jitar cewa ta kakaba haraji kan masu bukukuwan aure, suna da kuma masu jana'iza.

Source: Facebook
Gwamna ya musanta kakaba haraji kan jana'iza & aure
Kwamishinan yada labarai a jihar, Prince Dotun Oyelade shi ya karyata labarin a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.

Kara karanta wannan
"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyelade ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar a birnin Ibadan da ke jihar a ranar Alhamis 23 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki.
Har ila yau, Oyelade ya bukaci jama’a su yi watsi da wannan jita-jita inda ya ce an yi hakan ne domin tayar da hankulan al'ummar jihar kawai.

Source: Facebook
Ana zargin wasu na son bata sunan gwamnati
Oyelade ya ce an ƙirƙiri labarin ne domin bata sunan gwamnatin jihar, yana mai cewa duk wata sanarwa ta hukuma dole ta ƙunshi sa hannun shugaban hukumar haraji ta jihar.
Ya kuma bayyana cewa, wannan labarin bogi bai nuna adireshin ma'aikatar karbar haraji ta Oyo ba, wanda hakan ya tabbatar da cewa yaudara ne, cewar Daily Post.
Sanarwar ta ce"
“Babu ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗɗan da aka cika a cikin wannan saƙon da ya yadu game da cewa ana shirin karbar haraji kan aure da jana'iza.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana
“Haka kuma abu mai muhimmanci shi ne adireshin, wanda dole ne ya kasance daga ofishin tattara haraji ta jihar Oyo, amma wannan adireshin babu shi kwata-kwata a cikin saƙon yaudara.”
Gargadin gwamnatin Oyo ga al'umma, yan jarida
Kwamishinan ya gargadi ‘yan jarida da masu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da su daina yada labaran da ba a tabbatar da su ba kafin wallafawa.
Ya kara da cewa, yayin da zaɓe ke ƙaratowa, wasu ‘yan siyasa za su yi amfani da dabaru daban-daban don ɓata nasarorin da gwamnatin Seyi Makinde ta cimma cikin shekaru kusan bakwai da suka gabata.
Gwamna Soludo ya karyata shirin cafke malamai
Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Anambra ta yi martani kan rade-radin cewa tana shirin kama wasu malaman addinin Kirista a jihar.
Gwamna Charles Soludo ya karyata jita-jitar da ke cewa yana kokarin damke malaman addini, musamman Bishof-Bishof na Katolika.
Kwamishinan yada labarai, Dr. Law Mefor, ya ce labarin karya ne da aka kirkira domin tayar da hankalin jama’a da bata sunan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng