Shugaban INEC Mai Jiran Gado Ya Isa Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, An Samu Bayanai

Shugaban INEC Mai Jiran Gado Ya Isa Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, An Samu Bayanai

  • Shugaban INEC mai jiran gado, Joash Amupitan ya isa fadar shugaban kasa yayin da ake shirye-shiryen rantsar da shi yau Alhamis
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai jagoranci rantsar da Farfesa Amupitan, wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu a INEC
  • Rahotanni sun nuna cewa sabon shugaban INEC zai gana da daraktoci da manyan jami'an hukumar bayan kama aiki a hukumance

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya isa fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a safiyar Alhamis.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar zaben Najeriya

Farfesa Amupitan ya ziyarci fadar shugaban kasar ne domin karbar rantsuwar kama aiki daga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Farfesa Amupitan.
Hoton shugaban INEC mai jiran gado, Farfesa Josh Amupitan lokacin da ya isa fadar shugaban kasa Hoto: @oritokemedia
Source: Facebook

Channels tv ta ce Farfesa Amupitan, ya isa Aso Rock Villa a sanye da farin agbada da hula da ake kira zinariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban INEC ya isa fadar shugaban kasa

Bugu da kari, ya gaishe da masu kallo da jami’an fadar gwamnati kafin fara bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban INEC, mai alhakin shirya zabuka a Najeriya.

Wasu daga cikin hadiman shugaban ƙasa ne suka raka shi zuwa wajen taron, wanda aka tsara za a gudanar da shi da ƙarfe 1:00 na rana.

A gefe guda juma, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yana jagorantar taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) yanzu haka a ɗakin taro da ke Aso Rock.

An ruwaito cewa taron ya samu halartar gwamnonin jihohi 36 da mataimakansu da manyan mukarraban gwamnatin Najeriya, cewar rahoton Daily Post.

Shirin rantsar da shugaban INEC ya kankama

Sai dai kuma duk da haka Farfesa Amupitan zai karbi rantsuwar kama aiki a fadar gwamnati kamar yadda aka tsara a yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Atiku da wasu manya na fafutukar fito da shi, shugaban IPOB ya rikita lissafin lauyoyi a kotu

Hakan dai na zuwa ne mako guda da Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadinsa bayan tsauraran tambayoyi da tantancewa da aka yi masa ranar 16 ga Oktoba, 2025.

A yayin tantancewar, Amupitan, mai shekaru 58 ya bayyana tsarinsa na dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe na ƙasa, tare da inganta ayyukan INEC a cikin gida.

Farfesa Joach Amupitan.
Hoton Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan yayin tantance shi a Majalisar Dattawa Hoto: @Ayofe
Source: Twitter

Farfesa Amupitan, wanda Shugaba Tinubu ya naɗa kuma Majalisar Magabata ta Kasa ta amince da shi, ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa ya kare kwanan nan.

Bayan rantsar da shi, ana sa ran Amupitan zai shiga ofishinsa da ke hedkwatar INEC a Abuja domin ganawa da daraktoci da manyan jami'an hukumar zabe ta kasa.

Amupitan ya fadi sauyin da zai kawo a INEC

A wani rahoton, kun ji cewa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce zai tabbatar da sahihin zabe da zai sa wadanda suka fadi su yarda da rashin nasara.

Farfesa Amupitan ya ce zaben da zai rika shiryawa zai kasance wanda zai tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa da kowa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu zai rantsar da shugaban INEC na kasa, an ji abin da zai fara yi a ofis a Abuja

Ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi a Majalisar Dattawa lokacin tantance shi, ya ce burinsa samarda tsarin zabe mai inganci, wanda kowa zai yi na'am da shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262