Nnamdi Kanu: An Gano Abin da Buratai, Gwamnoni da Wasu Manyan Kasa za Su Fada a Kotu
- Nnamdi Kanu ya fitar da jerin shaidu yayin da ya ke shirin kare kansa a shari’ar ta’addanci da gwamnatin Najeriya ke yi da shi
- Cikin jerin akwai tsofaffin ministoci, hafsoshin tsaro da gwamnoni da suka hada da Abubakar Malami, T.Y. Danjuma da Tukur Buratai
- Shaidun za su bayar da bayani kan yadda aka kama Kanu, yadda aka haramta IPOB, da kuma abubuwan da wasu batutuwa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Sababbin bayanai sun fito kan irin shaidu da jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, zai gabatar domin kare kansa a kotu.
Gwamnatin Najeriya na shari’a da Nnamdi Kanu a kan zargin ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Source: Getty Images
Daily Trust ta wallafa cewa an raba shaidun wanda aka mika wa kotu a ranar 21 ga Oktoba, 2025 zuwa rukuni biyu.

Kara karanta wannan
Atiku da wasu manya na fafutukar fito da shi, shugaban IPOB ya rikita lissafin lauyoyi a kotu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An raba shaidun namdi Kanu
The Guardian ta wallafa cewa an raba wadanda Nnamdi Kanu ya ke son gabatar wa a gaban kotu zuwa rukuni na A, wadanda suka nuna sha'awar bada shaida.
Sai kuma rukuni na B, wadanda doka za ta tilasta su bayyana a gaban kotu bisa Sashe na 232 na dokar shaidu na shekarar 2011.

Source: Facebook
Cikin rukuni na biyu akwai tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN; tsohon Shugaban Hukumar DSS, Yusuf Bichi da tsohon Shugaban Hafsan Soja, Laftanar Janar Tukur Buratai (rtd).
Sauran sun hada da tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma (rtd); da tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.
Sai kuma Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu; Gwamnan Imo, Hope Uzodinma; tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu; Ministan Abuja, Nyesom Wike; da kuma Ministan Ayyuka, Dave Umahi.
Me shaidun za su ce a kotu?
A cewar takardun kotun, Abubakar Malami zai bayar da shaida kan matakan da suka shafi kamo Kanu a kasashen waje, yanayin tsare shi da kuma yadda aka bi dokokin kasa.

Kara karanta wannan
Kanu: Dan ta'addan da aka rike ya jero gwamnoni, ministocin Tinubu, Buhari a shaidu
Tukur Buratai zai yi bayani kan samamen da sojoji suka kai gidan Kanu a 2017, yayin da Dave Umahi zai yi jawabi kan haramcin IPOB.
Okezie Ikpeazu zai bayar da bayani kan rawar da gwamnatinsa ta taka lokacin samamen 2017, yayin da Hope Uzodinma zai yi magana kan kisan Ahmed Gulak da yadda rahotanni suka wanke IPOB daga laifin.
Nyesom Wike zai yi bayani kan rikicin Obigbo bayan zanga-zangar EndSARS, yayin da Babajide Sanwo-Olu zai yi shaida kan abin da ya faru a Lekki Toll Gate da rahoton kwamitin EndSARS.
Janar T.Y. Danjuma (rtd) zai yi bayani kan gargadin da ya taba yi a 2018 da ke cewa ‘yan Najeriya su kare kansu, wanda lauyoyin Kanu ke ganin yana tallafawa hujjar kare kai.
Haka kuma, akwai Bruce Fein da Barry Sutton, ‘yan ƙasar Amurka biyu, da za su yi bayani kan haramcin kama mutum ta hanyar tilasta wa da sauransu.
Nnamdi Kanu zai kare kansa a kotu
A baya, mun wallafa cewa a wani sabo mataki na shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar da kotu cewa ya shirya fara kare kansa daga ranar 24 Oktoba, 2025.
Ya mika takarda ranar 21 Oktoba wacce ya sa hannu domin bayyana adadin shaidu da zai kira — jimlar 23 — waɗanda aka raba zuwa rukuni biyu domin mika bayanai ga kotu.
Ya kuma roƙi kotun da ta ba shi ƙarin kwanaki 90 domin kammala kare kansa, duba ga adadin shaidu da muhimmancin hujjojin da zai gabatar a shari'ar da gwamnati ke yi da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
