Bola Tinubu Zai Rantsar da Shugaban INEC na Kasa, An Ji Abin da Zai Fara Yi a Ofis a Abuja

Bola Tinubu Zai Rantsar da Shugaban INEC na Kasa, An Ji Abin da Zai Fara Yi a Ofis a Abuja

  • Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da Farfesa Josh Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC gobe Alhamis
  • Wata sanarwa da ta fito daga INEC ta nuna cewa Amupitan zai gana da daraktoci da jami'an hukumar bayan kama aiki a hukumance
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa Amupitan ya maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya – Alamu na nuna cewa sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, zai kama aiki a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

Bayanai sun nuna cewa matukar ba a sanu wani sauyi ba, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da shugaban INEC a gobe Alhamis a Aso Rock.

Kara karanta wannan

'Za a yi sahihin zaben da kowa zai yi yarda da shi a 2027,' Shugaban INEC

Farfesa Amupitan.
Hoton shugaban INEC mai jiran gado, Farfesa Amupitan lokacin da ake tantance shi a Majalisar Datttawa Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Farfesa Amupitan shi ne wanda Shugaban Ƙasa ya naɗa domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu a hukumar INEC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta amince da nadin Amupitan

A makon jiya, Majalisar Dattawa ta tantance shi a zaman mambobi gaba daya maimakon tura batun zuwa kwamitin da ya dace kamar yadda aka saba.

Bayan rantsar da shi a fadar shugaban ƙasa, ana sa ran Farfesa Amupitan zai isa ofishin babbar sakatariyar hukumar INEC da ke Abuja da misalin ƙarfe 1:30 na rana

Bugu da kari, an samu labarin cewa zai yi ganawar farko da daraktoci da manyan jami’an INEC duk a gobe Alhamis, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Abin da shugaban INEC zai fara yi a ofis

Ana kyautata zaton a taron, za a bayyana masa halin da ake ciki kan shirye-shiryen zaben gwamna da za a gudanar a jihar Anambra ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

"Akwai matsaloli': Amupitan ya fadi shirinsa kan amfani da BVAS a zabukan Najeriya

Haka zalika zai ji inda aka kwana a shirin zaɓen ƙananan hukumomi na Abuja da aka tsara yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2026, tare da bayani game da rijistar masu zaɓe da ake gudanarwa yanzu haka.

Shugabar INEC ta rikon kwarya da sauran kwamishinoni za su halarci taron farko a ranar Alhamis.

Farfesa Amupitan da Bola Tinubu.
Hoton Farfesa Amupitan a ofishinsa na Jami'ar Jos da na Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Farfesa Amupitan zai gana da daraktoci

Hakan na kunshe a cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar INEC, Wilfred Ifogah, ya fitar a madadin Daraktan Ilimantarwa da Wayar da Kai a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce:

“Mai girma shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai gana da daraktoci ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 1:30 na rana.
"Za a yi wannan taro ne a babban ɗakin taro na hukumar INEC, Abuja. Saboda haka, ana gayyatar yan jaridar da ke aiki a INEC."

Amupitan ya fadi shirinsa idan ya karbi INEC

A wani rahooton, kun ji cewa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce zai tabbatar da sahihin zabe da zai sa wadanda suka fadi su yarda da sakamako.

Farfesa Amupitan ya ce zai yi aiki tare da hukumomi kamar hukumar NIMC da NCC domin tabbatar da ingantaccen tsarin zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Amupitan: Majalisa ta cin ma matsaya kan nadin sabon shugaban INEC da Tinubu ya yi

Ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi a zaman Majalisar Dattawa, ya ce INEC a karkashinsa za ta kawo gagarumin sauyi. Azabemmmmm

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262