"Kun Yi Kadan," Gwamna Abba Ya Aika Sako ga Masu Son Hada Shi Fada da Kwankwaso
- Gwamna Abba Yusuf ya ce babu wani mai mugun nufi da ya isa ya shiga tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 69 da haihuwar jagoransa, Kwankwaso, da aka gudanar a cikin jihar Kano
- Kwankwaso dai ya yi kira ga mambobin NNPP da Kwankwasiyya a fadin ƙasa su ci gaba da haɗa kan su don nasarar jam’iyyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake fitowa fili, ya fadi irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Abba Yusuf ya bayyana cewa babu wani dan hassada na cikin gida ko waje da zai iya raba shi da jagoransa kuma wanda ya zama garkuwarsa a siyasa, watau Kwankwaso.

Source: Twitter
'Ba mai raba ni da Kwankwaso" - Abba
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin bikin murnar cika shekaru 69 da haihuwar Kwankwaso, wanda aka gudanar a gidansa da ke Miller Road, Kano, a ranar Talata, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba wani makiyi, ko daga ciki ko daga waje, da zai iya shiga tsakaninmu. Duk karya suke yi, sun yi kadan su raba mu” in ji gwamna Yusuf.
Ya ce dangantakarsu da Kwankwaso za ta ci gaba da ƙarfafa, duk da shirin wasu da ke son ganin an samu sabani tsakaninsu.
“Jagoranmu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mutum ne mai hangen nesa, wanda Allah ya ba kyakkyawar zuciya da kishin ƙasa."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf.
“Zan daukaka akidar Kwankwasiyya” - Abba
Gwamna Abba Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da akidar Kwankwasiyya a cikin shirye-shiryen ci gaban jihar.
“Za mu ci gaba da tafiya a kan akidar Kwankwasiyya da ta haɗa da gaskiya, adalci da sadaukarwa wajen inganta rayuwar al’umma, za mu daukaka wannan akida."
- Gwamna Abba Yusuf.
Ya ƙara da cewa hadin kai tsakanin gwamnatin NNPP, jami’an gwamnati da mambobin Kwankwasiyya yana nan daram, duk da yunkurin masu neman raba kawunansu.

Source: Facebook
Sanata Kwankwaso ya yi kira ga haɗin kai
A nasa jawabin, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya taɓa zama gwamnan jihar Kano sau biyu, ya yaba da irin soyayyar da ake nuna masa daga mabiyansa da ’yan jam’iyyar NNPP.
Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da mabiyan Kwankwasiyya a fadin ƙasa su ci gaba da haɗa kai don tabbatar da nasarar jam’iyyar a gaba.
Kwankwaso ya kuma gode wa shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Ajuji Ahmed, da sauran mambobin jam’iyyar daga jihohi sama da 30 da suka halarci bikin.
Kanawa sun yi martani ga 'yan adawa
A zantawar Legit Hausa da Abba Hassan Gezawa, ya ce ya kamata mutane su gane cewa, alakar Kwankwaso da Abba ba irin ta tsohon gwamna ba.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
"Shi Abba dan amana ne, kuma ita amana sai dan amana. Muna da yakinin Abba ba zai butulcewa Kwankwaso kamar tsohon gwamna ba.
"Don haka mu Kanawa muna tare da Kwankwasiyya, kuma za mu bi Abba Yusuf har bayan 2027 don mun gama gane shi ya san halacci kuma ba zai ci amana ba."
- Abba Hassan.
Sagir Rabiu Zoo Road ya ce akwai bukatar 'yan adawar Kwankwasiyya su shafawa kansu ruwan sanyi, su bar Abba da Kwankwaso sai ta Allah ta yi.
"
Kwankwaso ya kafa tubalin jami’ar lafiya
A wani wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da ginin jami’ar koyar da likitanci ta farko mai zaman kanta a jihar Kano da garinsa na Kwankwaso.
An sanya wa jami’ar suna 'Jami'ar likitanci ta Nafisatu', wacce za ta samo tushe daga kwalejin fasahar aikin jinya ta Nafisatu, wanda Kwankwaso ya kafa a baya.
An ce wannan babban aikin ginin jami'ar zai zama wani babban ci gaba wajen horar da sababin likitoci da ma’aikatan lafiya a yankin Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

