Sarkin Musulmi Ya Nuna Yatsa ga Kasashen Yamma kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Batun zargin kisan Kiristoci da zaluntarsu a Najeriya na ci gaba da jawo muhawara a tsakanin kungiyoyin addinai
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya fito ya yi tsokaci kan lamarin da ake ta yadawa
- Ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin zargin wanda wasu daga kasashen Yammacin duniya ke ta yadawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa (NTRC), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi magana kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya karyata rade-radin cewa ana kisan kiyashi kan Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa wannan labari ne na karya da bai kamata a bar shi ya yadu ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a babban taron majalisar sarakunan Arewa na 2025, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, a ranar Talata, 21 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
Ta yi tsami tsakanin fadar shugaban kasa, kungiyar CAN kan zargin kisan Kiristoci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Sarkin Musulmi ya ce kan kisan Kiristoci?
Ya bayyana cewa zargin kisan Kiristocin wanda wasu a kasashen Yamma ke yadawa, ba komai ba ne face tsabagen karya.
“Wasu daga kasashen Yammacin duniya kamar Amurka da Canada suna ta yada labarin cewa ana kisan kiyashi kan Kiristoci a Najeriya. Ina kuma? A ina? Wadannan labarai ne na karya."
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III
Ya ce ba zai yiwu a ce ana irin wannan kisa a wani bangare na kasar nan, amma sarakuna ba su sani ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
Sarkin Musulmin ya bukaci shugabanni su dauki mataki wajen daidaita harkokin kafafen sada zumunta, saboda yadda wasu ke amfani da su wajen yada labaran karya da cin mutunci ga kasa da mutane.
Sarkin Musulmi ya bukaci a daina zagin sojoji
Sarkin Musulmi ya kuma roki ’yan Najeriya su daina zagin rundunar sojoji, yana mai cewa ba don sadaukarwar dakarun Najeriya ba, da kasar ba ta kasance da hadin kai da zaman lafiya irin na yanzu ba.

Kara karanta wannan
Zargin kisan Kiristoci: An 'gano' yawan coci, masallatai da aka ruguza a Najeriya
“Mun san akwai kalubale da kura-kurai a rundunar tsaro, amma kalaman da wasu ke yi a kafafen sada zumunta suna zarginsu da yin hadin baki da ’yan bindiga abin takaici ne kuma rashin adalci."
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Source: Facebook
Ya jaddada kudirin sarakunan gargajiya na goyon bayan ci gaban dimokuradiyya da biyayya ga shugabannin da aka zaba, daga shugaban kasa zuwa gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi da na kasa.
Sarkin Musulmi ya kuma bukaci sarakunan da suka halarci taron da su hada kai wajen fuskantar matsalolin da ke addabar kasa, yana mai cewa shawarwarin da aka cimma a taron za a mika su ga gwamnonin Arewa domin daukar matakin da ya dace.
MURIC ta karyata batun zaluntar Kiristoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkokin Musulmai ta Najeriya (MURIC) ta yi tsokaci kan zargin zaluntar Kiristoci.
Kungiyar ta nuna yatsa ga shugabannin Kiristoci na Najeriya kan yin amfani da Amurka don matsawa gwamnatin tarayya lamba.
Ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya kan zargin da ake yadawa cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyasa a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng