Kotu Ta Fadi Dalilin Dage Zaman Shari'ar Kwamandojin 'Yan Ta'addan Ansaru

Kotu Ta Fadi Dalilin Dage Zaman Shari'ar Kwamandojin 'Yan Ta'addan Ansaru

  • Kotu ta dage shari’ar manyan kwamandojin Ansaru da ake tuhuma da aikata laifuffukan ta'addanci da su ka keta hakkin 'yan kasa
  • Ana zargin su da jagorantar kungiyar ta’addanci, daukar nauyin ayyukan ta’addanci da satar mutane, lamarin da ya saba dokar kasa
  • Daya daga cikin su ya amsa laifin da ake tuhumarsu da aikata wa, kuma kotun ba ta bata lokaci ba wajen yanke masa hukunci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da shari’ar wasu manyan shugabannin kungiyar ta’addanci ta Ansaru.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da lauyan gwamnati, Mohammed Abubakar, ya kasa halartar zaman da aka sanya a ranar Talata.

Kotu ta dage shari'a da mayakan Ansaru
Hoton Shugaban Sojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Alkalin kotun, Emeka Nwite, ya ce lauyan ya aika da takardar neman afuwa tare da bayani kan dalilin rashin zuwansa.

Kara karanta wannan

DSS ta gano jihohi 2 da 'yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare hare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nemi dage shari'ar 'yan Ansaru

Business day ta wallafa cewa lauyan gwamnati, Mohammed Abubakar ya nemi kotu a dage zaman domin ya halarci shari’ar da kansa a zama na gaba.

Babu wani sabani daga bangaren lauyoyin wadanda ake tuhuma, hakan ya sa kotu ta dage shari’ar zuwa 19 ga Nuwamba domin fara sauraron karar.

Wadanda ake tuhumar sune Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar, wanda ya bayyana kansa a matsayin Sarkin Ansaru.

Sai kuma abokin aikinsa mai suna Mahmud al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda — mataimaki kuma shugaban ma’aikatan kungiyar.

An gurfanar da su a ranar Alhamis, 11 ga Satumba bisa tuhume-tuhume 32 da suka hada da ta’addanci da hada baki da kungiyoyin ta’adda.

Haka kuma ana zarginsu da jagorantar daukar matasa su shiga kungiyarsu tare da shirya hare-hare a fadin Najeriya.

Jagora a Ansaru ya amsa laifinsa

Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Abu Bara’a, ya amsa cewa yana gudanar da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kotun Koli ta shirya raba gardama kan dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Rivers

Ya kara da masa laifin amfani da kudin da yake samu wajen sayan makamai domin ta’addanci da satar mutane a sassan Najeriya.

Kotu za ta ci gaba da shari'ar mayakan Ansaru a Nuwamba
Hoton kofar daya daga cikin kotunan Najeriya Hoto: Getty
Source: UGC

Kotu ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru 15 saboda wannan laifi, tare da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar DSS.

Zai ci gaba da fuskantar sauran tuhumomi guda 31 da ake masa a wanna shari'a da ake gudanarwa a yanzu haka.

A baya, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana su a matsayin masu hannu dumu-dumu a harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje a 2022.

A wannan hari, sun yi nasarar kubutar da fursunoni sama da 600, daga cikinsu har da wadanda ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.

An gano shirin kai hari jihohin Najeriya

A wani labarin. mun wallafa cewa DSS ta bayyana cewa ta samu ingantattun bayanai kan wasu jihohi guda biyu da ke shirin fuskantar hare‑hare daga ƙungiyoyin ta’addanci.

Rundunar tsaron farin kayan ta bayyana cewa bayanan da ta samu sun tabbatar mata da cewa tattara mayaka da makamai domin aiwatar da mugun nufi a kan bayin Allah.

Kara karanta wannan

Trump ya gargaɗi Hamas kan yarjejeniyar Gaza, ya aika wakili Isra'ila

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a ya fitar, hukumar ta ce an gano yadda wasu ƙungiyoyi suke shirin amfani da wasu yankuna da tashoshin sufuri don kai farmaki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng