Zargin Kisan Kiristoci: An ‘Gano’ Yawan Coci, Masallatai da Aka Ruguza a Najeriya
- Kungiyar kare hakkin Musulmi ta yi magana kan zargin da ake yadawa kan cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya
- MURIC ta zargi shugabannin Kiristoci da amfani da Amurka wajen matsa wa gwamnati lamba domin nuna wariya ga Musulmai
- Farfesa Ishaq Akintola ya ce rahoton da wasu suka aika zuwa Amurka kan “kisan Kiristoci” yana nuni da wani boyayyen shiri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmai ta MURIC ta nuna damuwa kan yada cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Kungiyar ta zargi shugabannin Kiristoci na Najeriya da amfani da Amurka domin tsoratarwa da matsa wa gwamnatin tarayya lamba.

Source: UGC
Zargin kisan Kiristoci: Kungiyar MURIC ta magantu
A wata sanarwa da Farfesa Ishaq Akintola, daraktan kungiyar ya fitar da Daily Trust ta samu, ya bayyana cewa rahoton “kisan Kiristoci” ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce hakan na nuna yadda wasu ke ganin Amurka a matsayin ƙasar Kirista mai iko, maimakon su aika da rahoton zuwa ƙungiyoyin Afirka kamar AU ko ECOWAS.
Akintola ya ce kungiyar ta dade tana lura da ikirarin cewa Kiristoci ne kawai ake kashewa a Najeriya, wanda a cewarsa karya ce.
Ya ce Musulmai ma suna fuskantar kashe-kashe, amma labarinsu baya samun gurbi saboda kafafen yada labarai na Turawa da Kiristoci ke da rinjaye.
Farfesan ya bayyana cewa duka Kiristoci da Musulmai suna cikin barazanar ta’addanci, inda ’yan ta’adda ke kai hari kan coci-coci da masallatai da wuraren taro.
Ya ce a jihohin da Kiristoci suka fi yawa kamar Benue da Plateau, su ne ke rasa rayuka, haka nan Musulmai a Sokoto da Zamfara.
'Yawan coci da masallatai da aka rusa'
Farfesa Akintola ya ce yayin da majami’u kusan 200 suka ruguje a Arewa, masallatai sama da 6,000 ma sun rushe a yankin.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya fasa kwai kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
Kungiyar MURIC ta ce Musulmai a Kudancin Najeriya na fama da wariya ta tsarin gwamnati, inda koke-kokensu ke zama kamar ba a ji.
Ya kara da cewa rahotannin da aka aika zuwa Amurka wani yunkuri ne na tilasta gwamnati ta bai wa Kiristoci abin da bai kamata su samu ba.

Source: Twitter
Zargin MURIC kan kasar Amurka
Akintola ya zargi Amurka da matsin lamba kan kasashen Musulmai, yana mai cewa Kiristocin Najeriya na fakewa da hakan don cimma wata manufa.
Ya ce abin kunya ne a kai rahoton Najeriya ga Amurka, musamman ga shugaban kasar Donald Trump, wanda ya tallafa wa yaƙe-yaƙen kisan jama’a.
MURIC ta roƙi gwamnati kada ta amince da wannan “gugar zana ta Kiristoci” da ke neman mayar da Musulmai tamkar abin tsokana.
Minista ya magantu kan zargin kisan Kiristoci
Kun ji cewa ana ci gaba da muhawara kan batun yi wa Kiristoci kisan kare dangi da ake zargin ana yi a jihohin Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya sake fitowa ya karyata wannan zargin da ake yadawa.
Ministan ya bayyana cewa masu yada batun kisan Kiristocin suna yi ne don lalata hadin kan da ake da shi a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

