'Na Dauka Biri ne': Mafarauci Ya Bindige Mata har Lahira da Ya Hango Ta kan Bishiya

'Na Dauka Biri ne': Mafarauci Ya Bindige Mata har Lahira da Ya Hango Ta kan Bishiya

  • Rundunar yan sanda ta kama wani maharbi bayan ya dirkawa wata bindiga a cikin daji yayin da yake farauta
  • Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Boki da ke jihar Cross River inda ya harbe mace da kuskure yana zaton biri ne
  • Rahotanni sun nuna cewa bayan ya harba harsashi, sai ya ji ihun mutum sannan daga baya ya gano cewa mace mai suna Victoria ce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Boki, Cross River - Jami'an tsaro sun tsare wani maharbi a ƙaramar hukumar Boki ta Jihar Cross River bayan kuskuren harbe mata.

Maharbin ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya harbe matar bisa kuskure yana zaton biri ne a cikin daji yayin farauta.

Yan sanda sun kama maharbi da ya bindige mata a bishiya
Kwamishinan yan sanda a jihar Cross River, Rashid Afegbua. Hoto: Cross River Police Commanf.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Basam Osokom da ke Boki da ke jihar a ranar Litinin 20 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun je har gida, sun cafke malamin addinin Musulunci a jihar Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuskuren harbe mutane da mafarauta ke yi

Ana yawan samun matsala daga mafarauta kan bindige mutane har lahira bisa kuskure wanda ke jawo rasa rayukan mutane da dama.

Ko a shekarar 2022 ma wani maharbi ya yi kuskuren harbe wani jigo a APC har lahira wanda jami'an tsaro suka cafke shi daga baya.

Maharbin ya bindige tsohon shugaban jam'iyyar APC na wata gunduma a jihar Enugu bisa kuskure ranar Asabar 16 ga watan Maris 2022.

Yadda aka zargi Fulani da kashe dan APC

Jama'an gari sun ɗora wa Fulani makiyaya laifin, amma daga baya aka gano cewa wani mafarauci ne ya yi kisan bisa kuskure.

Hukumar yan sanda ta jihar ta ce tuni jami'ai suka fara bincike a sashin CID kasancewar lamarin ya shafi kisan kai domin tabbatar da daukar matakin da ya dace kan wanda ake zargi.

Mafarauci ya bindige mata da ya zaton biri ne
Taswirar jihar Cross River da ke Kudu maso Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda mafarauci ya bindige mata bisa kuskure

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun watsa daruruwan shanun sata 200 cikin gonaki, sun bukaci haraji

Maharbin mai suna Otu Goodness Kanang ya harbi matar da ya yi zato a matsayin biri, amma daga baya ya gano cewa mutum ya harbo.

Mutumin ya ce bayan ya yi harbin ne sai ya ji kuka inda ya duba sai ya ga ashe mace ce a kan bishiya ba biri ba kamar yadda yake tsammani.

Bayan da aka gano cewa marigayiyar mace ce mai suna Victoria, ‘yan sanda tare da matasan gari sun dauki gawarta zuwa gidan wani dagaci.

Daga nan ne kuma, rundunar ta tabbatar da fara bincike kan lamarin domin gano bakin zaren da kuma matakin da ya kamata a dauka.

Mafarauci ya harbe limami a Osun

A wani labarin mai kama da wannan, rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Osun ta kama wani mafarauci da ake zargi da kisan wani limamin kauye mai shekara 78.

Mafaraucin ya yi ikirarin cewa shi barewa ya hanga a daji ya kuma harbe ta da bindigarsa amma da ya tafi dauka sai ya ga limamin a kasa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Osun a wancan lokaci ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.