Na Ɗauka Barewa Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun

Na Ɗauka Barewa Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Osun ta yi holen wani mafarauci da ake zargi da kisan wani limamin kauye mai shekara 78
  • Mafaraucin ya yi ikirarin cewa shi barewa ya hanga a daji ya kuma harbe ta da bindigarsa amma da ya tafi dauka sai ya ga limamin a kasa
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike

Osun - Rundunar yan sanda a Jihar Osun ta kama wani mafarauci wanda ake zargi da bindige tare da kashe wani limamin kauyen Alagunan a karamar hukumar Aiyedaade, wanda ya yi zaton naman daji ne, The Punch ta rahoto.

Jaridar Vanguard ita ma ta rahoto cewa mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, ce ta sanar da hakan yayin holen wanda ake zargin a hedkwatar rundunar a Osogbo, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Na Ɗauka 'Barewa' Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun
Na Yi Zaton Naman Daji Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Ta ce:

"A ranar 17 ga watan Afrilu, misalin karfe 11.30 na safe, wani mai korafi daga Ogbere Oloba a Ibadan ya zo caji ofis inda ya ce wani mafarauci daga kauyensu ya bindige mahaifinsa, Adegun Yusuf, 78, limamin kauyen Alaguntan a Orile-Owu kuma ya mutu.
"Daga bisani an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifin da ake zarginsa.
"Ya yi bayanin cewa ya tafi farauta ne sai ya hangi Barewa a cikin daji kuma ya harbe ta da bindigarsa ta mafarauta.
"Ya yi mamakin da ya tafi ya dauki barewan, kawai sai ya tarar da Baba Liman a kasa. Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike."

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

Kara karanta wannan

Kaduna: Fuskokin Mutanen Da Aka Kama Kan Satar Tankar Mai Ɗauke Da Fetur Na N6.2m

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel