Biki Bidiri: An Daura Auren Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya ana cikin Tafiya a Jirgi
- Jarumin Nollywood a Najeriya, Shawn Faqua ya angonce da amaryarsa fitacciyar mai kawata wurin biki, Sharon Maduekwe
- An daura auren ne a cikin jirgin kasa da ke tsakiyar tafiya daga Legas zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo, lamarin da ya sa ya shiga tarihi
- Hukumar Kula da Sufurin Jiragen kasa ta Najeriya ta bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka daura aure ana cikin tafiya a jirgi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Najeriya, Shawn Faqua, da mai kawata wurin bukukuwa, Sharon Ifunanya Maduekwe, sun kafa tarihi a Najeriya.
Jarumi Shawn Faqua da Sharon sun kafa tarihi ne yayin da aka daura masu aure a cikin jirgin kasa da ke tsakiyar tafiya daga Legas zuwa Ibadan, jihar Oyo.

Source: Facebook
An daura aure cikin jirgin kasan Najeriya
Jaridar The Nation ta tattaro cewa wannan ne auren farko irinsa da aka daura a cikin jirgin kasa a tarihin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa ma’auratan sun maida ɗaya daga cikin taragon jirgin ƙasa zuwa filin bikin aure, inda suka kawata wurin da kyawawan furanni, fitilu, da kayan ado.
Bugu da kari, kawayen amarya da abokan ango da limaman da suka daura auren duk suna cikin wannan tarago a lokacin da jirgin ke tafiya daga Legas zuwa Ibadan.
Hukumar NRC ta tabbatar da auren
A wani saƙo da Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta wallafa a shafinta na sada zumunta watau X, ta ce:
"Kauna ta kara tabbata a cikin jirgin kasa, abubuwa na tafiya yadda ya kamata. An kafa tarihi na daura auren farko a cikin jirgin kasa da ke tsakiyar tafiya a Najeriya.
"Wannan shaida ce da ke nuna cewa tafiya na iya zama mai alheri kuma kyakkyawa, mai manufa."
Yadda mutane suka shaida daurin auren
Bikin auren ya jawo dumbin martani da yabo daga jama’a a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yaba da tunanin ma’auratan da kuma yadda suka ƙirƙiri hanya ta musamman wajen daura aurensu.
Wasu fitattun jaruman masana'antar fim ta Nollywood da shahararrun mutane kamar Stan Nze da Buchi Franklin sun halarci daurin auren a cikin jirgin, abin da ya ƙara wa bikin armashi da farin ciki.

Source: Facebook
Masu sharhi kan harkokin yau da kullum sun bayyana auren a matsayin sabon salo da ya haɗa al’ada da zamani.
A cewarsu, ma’auratan sun nuna cewa soyayya da aure ba dole sai a cikin babban zaure ko masallaci ba, ko a cikin jirgin ƙasa mai tafiya, ana iya rubuta tarihi.
Mawakiyar Najeriya na burin shiga daga ciki
A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar mawakiya a Najeriya Tiwa Savage ta bayyana damuwar da ta shiga game da son aure a rayuwarta.
Tiwa Savage ta bayyana cewa a shirye take ta zama mata ta biyu a gidan aure idan hakan ne hanyar da za ta samu mijin da zai girmama ta.
Ta ce sau da yawa tana tsintar kanta a matsayin 'Sugar Mummy' watau mace mai daukar nauyin saurayinta, abin da ta ce bata so ya ci gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


