Abin da China Ta Ce ga Gwamnatin Tinubu bayan Ceto Mutanenta da Aka Sace

Abin da China Ta Ce ga Gwamnatin Tinubu bayan Ceto Mutanenta da Aka Sace

  • Gwamnatin China ta yaba wa Najeriya bisa ceto ‘yan kasar hudu da aka sace a jihar Kwara ta hannun jami’an tsaro
  • Jakadan kasar China a Najeriya, Yu Dunhai, ya gode wa DSS da sojoji bisa gaggawar da suka yi wajen gano inda aka boye mutanen da aka sace
  • ‘Yan kasar sun samu kulawa ta musamman a asibitin DSS da ke Abuja bayan ceto su, abin da ofishin jakadancin China ya yaba da shi sosai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Jamhuriyar China ta yi magana bayan jami'an tsaro sun ceto wasu daga cikin mutanenta guda hudu da aka sace.

Kasar ta bayyana godiyarta ga gwamnatin Najeriya bisa nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen ceto ‘yan kasar China hudu da aka sace a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

China ya yabawa kokarin gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro
Shugaba Bola Tinubu da jakadan China a Najeriya, Yu Dunhai. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

China ta yabawa jam'ian tsaron Najeriya

An gudanar da aikin ceton ne tare tsakanin Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hukumar DSS, da rundunar sojojin Najeriya, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jakadan kasar China a Najeriya, Yu Dunhai, ya bayyana hakan ne a wurin mika wadanda aka ceto a asibitin DSS da ke Abuja a ranar Lahadi 19 ga watan Oktoban 2025.

Ya yabawa DSS bisa saurin da suka nuna wajen amfani da basira wajen gano da kuma kubutar da ma’adinan kasar China lafiya.

China ta yabawa Ribadu da jami'an tsaro kan ceto mutanenta
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Sunayen yan China da aka ceto a Kogi

‘Yan kasar China da aka ceto su ne Dansu Zhou, Zhou Hai, Zhou Jia Jun, da Fan Xiu Guo, wadanda aka sace a hanyarsu ta zuwa ma’adinan Saminaka a karamar hukumar Yagba ta Yamma ta jihar Kogi.

An ce ‘yan bindiga bakwai dauke da AK-47 ne suka tare su kafin jami’an tsaro su bi sahunsu su ceto su lafiya, kamar yadda Zagazola Makama ta ce.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar juyin mulki, an gargadi masu zanga zanga kusantar fadar Tinubu

Jakadan ya kuma yaba da kulawar likitocin DSS ga wadanda aka ceto, inda ya bayyana asibitin na Abuja a matsayin mai inganci da kayan zamani.

Ya ce:

“Bayan an ceto su, jami’an DSS sun garzaya da su zuwa cibiyarsu don binciken lafiya kafin a kai su ofishin jakadancinmu.”

Rahotanni sun nuna cewa DSS na ci gaba da kai samame a jihohi daban-daban domin murkushe kungiyoyin masu laifi da ke tada hankalin kasa.

A baya-bayan nan, hukumar ta DSS ta samu yabo bayan ta kama manyan bindigogi da harsasai a Asaba da ke jihar Delta, abin da aka bayyana a matsayin nasara wajen yaki da rashin tsaro a Najeriya.

Sojoji sun kwato yan China da aka sace

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya ta ceto mutane 21 da aka sace a kwanan nan, ciki har da wasu ‘yan kasar China guda hudu a jihar Kwara.

An kaddamar da farmakin ne a karkashin Operation FANSAN YAMA domin murkushe ‘yan bindiga a Arewa ta Tsakiya.

Rundunar sojojin ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga, tare da hadin gwiwa da NAF da sauran hukumomi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.