Bello Turji Ya Saki Sama da Mutum 100 a Sabon Shirin Ajiye Makami da Daina Yaki
- An tabbatar da cewa dan ta'adda, Bello Turji ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a yankin Zamfara
- Rahoto ya ce hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin jagoran ‘yan bindigar da shugabannin al’umma a jihar
- Hukumomi sun ce suna sa ido sosai don tabbatar da cewa dan ta'addan bai sake daukar makami ba bayan sulhun
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a wani sabon yunkuri na samar da zaman lafiya da kawo karshen tashin hankali a Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa sakin wadannan mutanen ya biyo bayan dogon tsarin tattaunawa da amincewa da shirin sulhu da ake gudanarwa a wasu yankanan Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa wadanda aka sako sun hada da maza, mata da yara, kuma an mika su ga hukumomin yankin kafin kai su asibiti domin binciken lafiya da kulawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da ya sa Bello Turji sakin mutane
Majiyar tsaro ta shaida cewa wannan mataki na Bello Turji ya samo asali ne daga sakamakon tattaunawa mai zurfi tsakanin kungiyarsa da shugabannin al’umma da masu shiga tsakanin.
Wata majiya da ta shiga cikin tattaunawar ta bayyana cewa an fara sakin mutane 36, sannan daga baya aka kara sakin wasu takwas, wanda ya kai jimillar 46 a matakin farko.
Daga baya kuma aka ci gaba da sakin sauran, har adadin da aka sako ya kai sama da mutum 100 baki daya.
Majiyar ta kara da cewa ana sa ran karin sakin mutane cikin kwanaki masu zuwa yayin da tattaunawa ke ci gaba.
Yadda ake kokarin sulhu da Turji
Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin al’umma ne suka jagoranci wannan sabon shirin sulhu tare da taimakon jami’an tsaro da masu shiga tsakanin daga shiri.
Tsarin yana nufin samun amincewa tsakanin bangarorin domin kawo karshen daukar makami da satar mutane da ke addabar yankin.

Source: Facebook
Daya daga cikin masu sulhun ya ce wannan na iya zama babban mataki na farko wajen kawo karshen rikice-rikicen da suka dade suna hana al’umma zaman lafiya a Zamfara da kewaye.
Sai dai wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan yunkuri ba wajen ganin an yi sulhu da Bello Turji ko 'yan bindiga masu kai hari kan al'umma ba.
A wannan karon, an ce za a saka ido domin tabbatar da cewa dan ta'addan da mabiyansa ba su sake daukar makami ba bayan sulhun.
An ceto mutane a Kwara da Kogi
A wani labarin, mun rahoto cewa dakarun sojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihohin Kwara da Kogi.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa an ceto mutane sama da 20 bayan fafatawar da aka yi da 'yan ta'addan a cikin daji.
Mutanen da aka ceto sun hada da maza da mata kuma 'yan ta'addan sun jikkata su sosai ta yadda wasu daga cikinsu ba su iya tafiya da kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


