Juyin Mulki: ACF da Afenifere Sun Aika Sako ga Sojojin Najeriya

Juyin Mulki: ACF da Afenifere Sun Aika Sako ga Sojojin Najeriya

  • Kungiyoyin Afenifere da Arewa Consultative Forum (ACF) sun yi kira da a kare mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya
  • ACF ta bukaci ‘yan ƙasa su kwantar da hankula bayan rahoton yunkurin juyin mulki da ake ta yada wa a kwanakin nan
  • Ita kuma Afenifere ta ce babu wani dalili da zai sa soja su karɓi mulki, domin hakan zai mayar da Najeriya baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wasu manyan kungiyoyin shiyyoyin Najeriya, ciki har da Afenifere, Middle Belt Forum da ACF, sun bayyana cewa babu ɗan Najeriya mai son ganin soja ya sake karɓar mulkin kasar.

Kungiyoyin sun jaddada cewa lokaci ya yi da ya dace a bar dimokuraɗiyyar ƙasar ta girma da bunkasa domin samun ci gaban da ake bukata.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin APC ta jawo yunwa da matsalar tsaro a Najeriya, ADC ta fasa kwai

ACF da Afenifere sun damu kan batun juyin mulki
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sojoji suna masa fareti Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Leadership ta wallafa cewa tsohon sakataren ACF, Anthony Sani, ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa game da yiwuwar juyin mulki ba su da tabbas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Juyin mulki: ACF ta yi kira ga sojoji

Anthony Sani ya bukaci sojoji su baiwa tsarin dimokuraɗiyya dama ta yi bunkasar da kowa zai ji dadin tsarin.

Ya ce:

“Muna fatan cewa karyata labarin da rundunar soji ta yi gaskiya ne, domin idan aka yi juyin mulki yanzu, zai rusa cigaban da muke samu a hankali."

A cewarsa, Najeriya ta fara ganin cigaba a tsarin mulkinta, saboda haka ya kamata a bar wannan tsarin ya girma domin inganta rayuwar jama’a.

ACF ta bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankula, su kuma jira ƙarin bayani kan labarin kama wasu manyan hafsoshin soja da ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulki.

Kakakin ACF, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya ce har yanzu kungiyar ba ta yanke matsaya ba domin rahotannin da ke yawo sun saba wa juna, amma za a jira gwamnati.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin juyin mulki har Tinubu ya soke bikin ranar 'yanci? An samu bayanai

Afenifere: Babu dalilin yin juyin mulki

Kungiyar Afenifere ta karyata duk wani yunkurin juyin mulki, tana mai cewa hakan zai mayar da Najeriya shekaru baya.

Sojoji sun karyata zargin juyin mulki
Wasu daga cikin sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Getty Images

Kakakin Afenifere, Kwamred Jare Ajayi, ya ce tsarin mulki ya bayyana cewa babu yadda gwamnati za aa canja sai ta hanyar doka.

Ya ce:

“Mulkin soja yana soke kundin tsarin mulki kuma yana tauye ‘yancin ɗan adam. Abin farin ciki ne cewa tun 1999 Najeriya ke samun ci gaba a mulkin farar hula."

Ya ƙara da cewa ko da yake ƙasar na fuskantar ƙalubale, mulkin soja ba zai kawo mafita ba, sai ma abubuwa su ƙara tabarbarewa.

Ya yi gargadi ga duk wani soja mai niyyar juyin mulki da ya daina, domin irin wannan yunƙuri ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Afenifere ta yaba da sanarwar mai magana da yawun rundunar soji, Janar Tukur Gusau, wanda ya tabbatar da cewa babu wani yunkurin juyin mulki.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Ana zargin tsohon Gwamna da shirin juyin mulki

A baya, mun wallafa cewa majiyoyi daga rundunar tsaro sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna da ake zargi da hannu a shirin yin juyin mulki.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama wasu hafsoshin rundunar soji guda 16 saboda ana tuhumar su da shirin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

An bayyana cewa tsohon gwamnan na daga cikin wanda ake zargi da bayar da kudi domin taimakawa yunkurin da aka sa ranar aiwatarwa ita ce 25 ga Oktoba 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng