Kudirori 6 da Tinubu Ya Yi Fatali da Su, Ya Ki Rattabawa Hannu Su Zama Doka

Kudirori 6 da Tinubu Ya Yi Fatali da Su, Ya Ki Rattabawa Hannu Su Zama Doka

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ki amincewa da wasu kudirori da majalisar tarayya ta gabatar masa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Mai girma Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirorin ne tare da kin rattaba musu hannu don su zama doka a karkashin kundin tsarin mulki.

Shugaba Tinubu ya ki amincewa da wasu kudirori
Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Tinubu ya ki rattaba hannu kan wasu kudirori

Legit Hausa ta yi duba kan wasu kudirori akalla guda shida da Shugaba Tinubu ya ki rattabawa hannu su zama doka, bayan sun samu amincewa a majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasan yana bayyana dalilan da suka sanya ya ki amincewa da kudirorin da majalisa ta gabatar masa don rattaba hannu.

1. Kudirin tsawaita lokacin ritayar ma'aikatan majalisa

Shugaba Bola Tinubu ya ki rattaba hannu kan kudirin da ke neman tsawaita lokacin aikin ma’aikatan majalisar dokoki ta kasa daga shekaru 35 zuwa 40, tare da kara shekarun ritaya daga 60 zuwa 65.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi karin haske kan bukatar dawo da zaben 2027 zuwa 2026

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa an amince da kudirin ne a majalisar dattawa da majalisar wakilai a watan Fabrairu, amma wasu kungiyoyi ciki har da kungiyar ma’aikatan majalisa ta kasa (PASAN) sun soki kudirin.

Shugaba Tinubu ya ce ya yanke shawarar kin amincewa da kudirin ne bayan zurfin nazari da shawarwari.

2. Kudirin kafa jami’ar ilmi ta tarayya Numan (Adamawa)

Shugaba Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirin da ke neman kafa jami’ar ilmi ta Tarayya a Numan, jiihar Adamawa.

Jaridar The Punch ta ce an amince da kudirin a daukacin majalisun dokokin kasa a shekarar 2024.

Shugaban kasa ya nuna cewa akwai kurakurai da dama cikin kudirin, ciki har da tanadin da ya ba gwamnan jiha ikon mallakar filin jami’ar maimakon shugaban kasa.

3. Kudirin kafa asusun dakin karatu na majalisa

Shugaba Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirin da ke neman kafa asusun dakin karatu na majalisar dokoki ta kasa, 2025.

Idan za a iya tunawa, Premium Times ta kawo rahoto cewa kudirin ya samu amincewa a dukkan majalisar dattawa da ta wakilai.

Shugaban kasa ya bayyana cewa duk da cewa kudirin yana da manufofi masu kyau, wasu sassansa na karo da dokokin da ake aiki da su a yanzu.

Kara karanta wannan

Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi

4. Kudirin gyaran dokar kafa hukumar NDLEA

Shugaba Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirin gyaran dokar kafa hukumar NDLEA, 2025, wanda majalisa ta amince da shi.

Kudirin da aka ki amincewa da shi ya tanadi ba NDLEA ikon rike wani kaso daga kuɗi da aka kwato daga laifuffukan miyagun kwayoyi, sabanin tsarin dokar na yanzu.

Jaridar Nairametrics ta ce Shugaba Tinubu ya ce wannan kudiri ya sabawa Sashe na 58, sakin layi na 4 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

Ya bayyana cewa a karkashin dokar da ake da ita yanzu, duk kuɗin da aka kwato daga ayyukan laifi dole ne a ajiye su cikin asusun gwamnatin da ke kula da dukiyoyin da aka kwace.

Kudirin NDLEA na 2025 ya nemi kirkirar sabon tanadi, Sashe na 46(4) wanda ya ce hukumar za ta rike wani kaso daga kuɗaɗen da aka kwato yayin ayyukanta.

Shugaba Tinubu ya ki rattaba hannu kan wasu kudirori
Shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

5. Kudirin kafa cibiyar fasahar sufuri ta Najeriya

Kara karanta wannan

Amupitan: Majalisa ta cin ma matsaya kan nadin sabon shugaban INEC da Tinubu ya yi

Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da Kudirin kafa cibiyar fasahar sufuri ta Najeriya, 2025 da aka sabunta, wanda majalisa ta amince da shi.

Vanguard ta ce shugaban kasan ya ce ba zai iya sanya hannu ba, saboda akwai manyan matsaloli da rashin daidaito da tanade-tanaden kudi da kundin tsarin mulki.

Ya kara da cewa wasu sassan kudirin sun sabawa dokokin da ke aiki yanzu, kuma suna iya haifar da cin hanci ko amfani da kuɗi ba bisa ka’ida ba.

6. Kudirin kafa asusun dakin karatu na kasa

Shugaba Bola Tinubu ya ki amincewa da kudirin kafa asusun dakin karatu na kasa 2025, inda ya ce kudirin ya yi sabani da wasu dokoki da manufofin gwamnati.

A cewarsa, kudirin ya sabawa muhimman manufofin gwamnati kan batutuwan tattalin kuɗin hukumomin gwamnati, haraji, albashi da iyakar shekarun aiki ga ma’aikata.

The Cable ta ce Shugaba Tinubu ya ce amincewa da kudirin a haka zai kirkiro wani tsarin da ba zai dore ba, wanda zai iya zama barazana ga maslahar jama’a.

Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta cika baki kan tazarcen Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mai girma Bola Tinubu ta amince a kafa sababbin jami'o'i masu zaman kansu.

Amincewa da kafa sababbin jami'o'in zai kara yawan cibiyoyin ilimi na gaba da sakandire da ke hannun ‘yan kasuwa zuwa matakin da ba a taba gani ba.

Ministan ilmi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa an amince da kafa sababbin jam'o'in ne yayin taron majalisar zartaswa ta kasa (FEC).

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng