Jami'an Tsaro Sun Je har Gida, Sun Cafke Malamin Addinin Musulunci a Jihar Kwara
- Hukumar NSCDC ta kama wani Alfa mai suna Folorunsho Olaoti a Ilorin bisa zargin lakadawa yaro mai shekara 10 dukan tsiya
- An ce malamin ya fusata ne bayan yaron ya faɗa wa mahaifiyarsa cewa wani ya zage ta, lamarin da ya kai ga mummunan duka
- Gwamnatin Kwara ta ceto yaron kuma tana shirin gurfanar da Alfa a kotu, yayin da yaron ke samun kulawar likitoci a asibiti
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara – Rundunar tsaron farar hula (NSCDC) ta tabbatar da kama wani malamin addinin Musulunci mai suna Folorunsho Olaoti, a jihar Kwara.
Ana zargin malamin da lakadawa wani yaro dan shekara 10 da ke zaune da shi dukan tsiya har ya raunata shi a unguwar Akerebiata, karamar hukumar Ilorin ta Gabas.

Kara karanta wannan
'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure

Source: Facebook
Malami ya lakadawa yaro duka a Kwara
Jaridar The Punch ta rahoto cewa cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025, bayan malamin ya zargi yaron da faɗa wa mahaifiyarsa cewa wani ya zage ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kara da yaron ya kai ya fusata malamin, wanda a cewar mazauna yankin, ya lakada wa yaron duka mai tsanani har sai da ya ji masa raunuka a jiki.
Majiyoyi sun ce, malamin da aka fi kira da Alfa a yankin ya kasance dan uwa ne ga mahaifin yaron, wanda ya rasu, kuma tun bayan mutuwarsa ne yake kula da yaron.
Sai dai a cewar mazauna yankin, ya dade yana zaluntar yaron, inda aka ce yana duka da wahalar da shi saboda dalilai marasa tushe.

Source: Original
Jami'an tsaro sun cafke malamin addinin
A tattaunawarta da manema labarai, Antonia Oshiniwe, sakatariyar Hukumar Aiwatar da Dokar Kariya ga Yara (CRIC) ta jihar Kwara, ta ce ta samu kiran gaggawa daga wani wanda ke anguwar, wanda ya roki a ceto yaron.
“Na samu kiran wani mutum da ya nemi taimako saboda yaron yana cikin mawuyacin hali. Na tafi wajen da abin ya faru, na tabbatar da gaskiyar abin, sannan na sanar da jami’an NSCDC, suka kama malamin a ranar Juma’a."
- Antonia Oshiniwe.
Antonia ta bayyana cewa yanzu an ceto yaron, kuma yana karkashin kulawar gwamnati tare da samun jinya saboda raunukan da ya samu.
NSCDC ta tabbatar da kama malamin addini
Ta ce gwamnati za ta gurfanar da malamin a kotu bisa zargin cin zarafin yaro, duka da kuma karya dokokin kare yara.
Mai magana da yawun hukumar NSCDC a Kwara, Ayoola Michael, ya tabbatar da kama wanda ake zargi, yana mai cewa rundunar ta fara cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya da adalci.
“Mun kama wanda ake zargi kuma bincike na gudana. Za mu tabbatar da cewa an gurfanar da shi, domin ba za a lamunci irin wannan dabi’a ba."
- Ayoola Michael.
Za a rataye malamin Musulunci a Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta yanke wa Malam Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe dalibar kwaleji.
Amma Mai shari’a Hannah Ajayi ta wanke wasu mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan Hafsoh Lawal, saboda rashin shaidu da hujjoji masu karfi.
Rahotanni sun nuna cewa Malam Abdulrahman ya kashe Hafsoh ne domin yin tsafi da ita don samun kudi da kuma safarar sassan jikinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

