Matasa Sun Taso Shugaba Tinubu a gaba, Suna So a Tsige Mamba a Hukumar NDDC

Matasa Sun Taso Shugaba Tinubu a gaba, Suna So a Tsige Mamba a Hukumar NDDC

  • Ƙungiyar matasan masu hakar mai ta COPYOS ta nemi a cire Otito Ehinmore daga wakilcin jihar Ondo a hukumar NDDC
  • COPYOS ta rubuta wa Shugaba Tinubu wasiƙa, tana zargin Ehinmore da fifita ‘yan uwansa, da kuma karkatar da kudi
  • Ƙungiyar ta ce idan Tinubu bai tsige Ehinmore cikin makonni biyu ba, za su gudanar da zanga-zanga da rufe ayyukan NDDC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo – Gamayyar kungiyar matasan jihar Ondo (COPYOS) ta nemi a cire Otito Ehinmore, wakilin jihar Ondo a hukumar raya yankin Niger Delta (NDDC).

Matasan da suke kiran kansu da sunan 'matasan da ke samar da mai' sun zargi Otito Ehinmore da cin hanci, almundahana, da rashin iya wakilci nagari.

Matasa sun bukaci Tinubu ya tsige wani mamba a hukumar NDDC
Shugaba Bola Tinubu ya na rattaba hannu kan takarda a filin wasa na Eagle Square Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

NDDC: Matasa sun aika bukata ga Tinubu

A cewar ƙungiyar, an aika da wannan buƙata ne cikin wata wasiƙa da aka rubuta wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai kwanan wata 15 ga Oktoba, 2025, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

A cikin wasikar, sun shaidawa Shugaba Bola Tinubu cewa sun ba shi wa’adin mako biyu don cire Ehinmore daga mukaminsa na mamba a NDDC.

An rahoto cewa fiye da matasa 30 daga yankunan da ke da albarkatun mai a jihar Ondo ne suka sanya hannu kan wannan wasika.

Matasan sun zargi Otito Ehinmore da nuna son kai, cin hanci, da rashin aiwatar da ayyukan raya jiha tun bayan nadinsa a hukumar NDDC.

Sun bayyana cewa tun lokacin da aka naɗa shi, “Ehinmore ya mayar da kujerar wakilin Ondo a hukumar NDDC tamkar marar amfani,” inda suka ce ba a ganin aikinsa ko gudunmawarsa ga ci gaban yankin.

Zargin fifita ‘yan uwa da karkatar da kudade

Kungiyar COPYOS ta kara zargin cewa Ehinmore ya bai wa ‘yan uwansa hud’u damar samun kujerun aiki guda hudu da aka ware wa yankunan da ake hakar mai a jihar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi hanya 1 da APC za ta iya lashe zaben gwamna a jihar Oyo

Sun bayyana sunayen su da: Dare Ehinmore, Dayo Ehinmore, Babatunde Ehinmore, da Taye Stella Olayemi.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta zarge shi da karkatar da wasy kudade da aka ware don shirye-shiryen tallafa wa matasa na shekarun 2023 da 2024.

Sannan sun zargi mamban da kuma rashin tuntubar shugabannin gargajiya da kungiyoyin matasa a kananan hukumomin Ilaje da Ese-Odo, inda ake hakar mai a jihar.

Matasa a Ondo sun zargi wani wakilinsu a hukumar NDCC da cin hanci da karkatar da kudade.
Taswirar jihar Ondo, daya daga cikin masu samar da fetur a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gargadin matasa ga gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba siyasa ce ta sanya suke son a tsige Ehinmore ba, kawai suna so a wanzar da gaskiya da samar da ingantaccen wakilci a cikin NDDC.

Sun gargadi Shugaba Tinubu da cewa idan bai cire Ehinmore cikin mako biyu ba, za su shirya zanga-zanga da rufe dukkanin ofisoshin NDDC a jihar Ondo, inji rahoton Business Day.

A cewar COPYOS:

“Ba za mu ci gaba da nade hannuwanmu muna kallon irin abin da Ehinmore yake yi na rashin kyautatawa ba. Lokaci ya yi da za a samu sauyin wakilci a NDDC."

Kara karanta wannan

MCAN: 'Yan NYSC Musulmi sun yi taron Arewa maso Gabas a Gombe

Sai dai a martaninsa, Otito Ehinmore ya karyata zarge-zargen, yana mai cewa siyasa ce kawai ke tattare da bukatar matasan.

Tinubu ya sauya wakilin Ondo a NDDC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya amince da maye gurbin wakilin Ondo a hukumar NDDC, Mista Victor Akinjo, da Hon Otito Atikase.

Fadar shugaban kasar ta sanar da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne daga ranar Juma'a, 1 ga watan Agusta, 2023, don samar da wakilcin Ondo a NDDC.

Shugaban kasar ya kuma amince da gaggauta maye gurbin wakilin Cross River a NDDC, Mista Asi Oku Okang, da sabon wakili, Rt. Hon. Orok Otuk Duke.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com