An Shiga Tashin Hankali: 'Yan Bindiga da Makiyaya Sun Mamaye Gari Guda a Benue

An Shiga Tashin Hankali: 'Yan Bindiga da Makiyaya Sun Mamaye Gari Guda a Benue

  • Rahotanni sun bayyana cewa makiyaya da ‘yan bindiga sun kafa sansanoni a wani gari da ke karamar hukumar Ukum
  • Mazauna wannan gari sun bayyana cewa ba sa iya yin noma ko fita kasuwa saboda tsananin tsoron hare-haren miyagun
  • Wannan na zuwa ne yayin da rundunar tsaro ta rusa sansanoni biyar na ‘yan bindiga a yankin Ukum da ke jihar Benue

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Tashin hankali ya karade garin Dyom, da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue, bayan rahotannin cewa wasu makiyaya dauke da makamai da ‘yan bindiga sun mamaye gonaki da gidaje a yankin.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kafa sansanoni a cikin da kewayen garin, suna kuma boyewa cikin gonaki idan jami’an tsaro ko ‘yan sa kai na Anyam Nyor suka bayyana.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

'Yan bindiga sun mamaye wani gari da ke cikin karamasr hukumar Ukum, jihar Benue
Taswirar jihar Benue da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin yankin, Terhile Uma, ya bayyana halin da suke ciki a matsayin abin tsoro da rashin tabbas a zantawarsa da jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gidajenmu suna kusa da Dyom. Idan suka ji cewa sojoji ko jami’an Anyam Nyor sun iso, sai su gudu su boye cikin gonakinmu. Ba mu iya fita, noma ko cin abinci cikin nutsuwa. Wannan wane irin zalunci ne?”

- Terhile Uma.

'Yan bindiga sun mamaye garin Benue

Rahotanni sun nuna cewa mutanen garin da dama sun bar gidajensu saboda tsoron harin ramuwar gayya daga ‘yan bindiga.

Wasu kuma sun makale a gidajensu cikin tsananin tsoro, yayin da harkokin noma da kasuwanci suka tsaya cak.

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Sun fara tilasta mutane biyan haraji a ranakun kasuwa kamar yadda tsohon shugaban ‘yan bindiga, Terwase Agwaza (Gana), ya saba yi."

Wani mazaunin yankin ya kara da cewa:

“Ba mu da tabbacin ko za mu tsira tsira. Har da rana ma cikin firgici muke, saboda suna yawo dauke da makamai a kowane lokaci.”

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a wani yankin Kaduna, an kashe fiye da mutane 5 a rana 1

‘Yan sanda ba su da rahoto a hukumance

Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Benue, DSP Edem Edet, ta ce ba ta samu cikakken rahoto kan lamarin ba tukuna.

Sai dai shugabannin al’umma sun bukaci gwamnatin jihar da rundunonin tsaro da su hanzarta daukar mataki.

“Ba mu da tsaro a yanzu. Idan gwamnati ba ta dauki mataki ba, mutane za su bar yankin baki daya,” in ji wani dattijo mai suna Tersoo Aondo.
Sojoji sun ragargaji sansanonin 'yan ta'adda a Benue
Hoton dakarun sojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An rusa sansanoni 5 na ‘yan bindiga

A yayin da ake fama da wannan barazana, rahotanni daga Sankera axis na Ukum sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kai samame tare da rusa sansanoni biyar na ‘yan bindiga.

Wani rahoto daga Zagazola Makama ya bayyana cewa, aikin ya gudana ne da hadin gwiwar ‘yan sanda, Operation Zenda, PMF, SIS da rundunar tsaron Benue (BCPG).

“Mun samu nasarar rusa sansanoni biyar bayan artabu mai tsanani. Mun kwato bindigar AK-47 daya da harsasai biyar. ‘Yan bindigar sun tsere da raunukan harbi.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

- In ji majiyar tsaro.

'Yan bindiga sun mamaye Benue - Gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana damuwa kan matsalolin tsaro da ke kara tsananta a jihar Benue, musamman da damina.

Hyacinth Alia Ya ce wasu miyagu na ƙoƙarin korar jama'a daga garuruwansu domin su mamaye su, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta kai masu dauki.

Gwamnan Benue ya gargadi 'yan siyasa da ke amfani da rikicin, ya kuma ce duk wanda ya yi laifi dan ta’adda ne kuma za a tona asirinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com