Biki Bidiri: Hotunan Auren Kanin Ministan Tinubu da Ya Auri Kanwar Gwamna

Biki Bidiri: Hotunan Auren Kanin Ministan Tinubu da Ya Auri Kanwar Gwamna

  • Ɗan’uwan minista a gwamnatin Bola Tinubu ya daura aure da yar gwamnan jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya
  • Kanin ministan ayyuka, Injiniya Silas Umahi ya angwance ne da yar gwamnan mai suna Cynthia Rebecca Nwifuru
  • An gudanar da bikin ne na gargajiya a fadar Sarkin Oferekpe Agbaja a ƙaramar hukumar Izzi da ke jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Manyan yan siyasa da al'umma da dama sun shaida daurin auren kanin minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Ɗanuwan Ministan Ayyuka, Injiniya Silas Umahi, ya ɗaura aure da yar gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru a fadar Sarkin Oferekpe.

An sha bikin kanin minista d akanwar gwamnan Ebonyi
Gwamna Francis Nwifuru da Dave Umahi yayin daurin auren yan uwansu. Hoto: Senator Engineer David Nweze Umahi, CON.
Source: Facebook

Kanin minista ya angwance da kanwar gwamna

Minista Dave Umahi shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Asabar 18 ga watan Oktobar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

‘Yar’uwar Gwamnan Jihar, Cynthia Rebecca Nwifuru ta zama amaryar Silas ne a bikin aure na gargajiya da aka gudanar a Oferekpe Agbaja, ƙaramar hukumar Izzi ta jihar.

A cewar Minista Dave Umahi, soyayyar ma’auratan ta fara ne a shekarar 2020, lokacin da babu wanda ya san da ita.

A cikin rubutunsa, Umahi ya ce:

"Jiya na halarci bikin auren gargajiya na Injiniya Silas Umahi da Rebecca Cynthia Nwifuru a fadar Mai Martaba Ezekiel Nwifuru Nwakpu, da ke Oferekpe Agbaja, ƙaramar hukumar Izzi.
Wannan aure gaskiya ikon Allah ne. Abin mamaki, dangantakar su ta fara a hankali tun shekarar 2020, kafin ko ɗaya daga cikin iyalansu ya sani."
An daura auren kanwar gwamna da kanin minista a Ebonyi
Hotunan daurin auren kanin Umahi da kanwar Gwamna Nwifuru. Hoto: Senator Engineer David Nweze Umahi, CON.
Source: Facebook

Umahi ya yi addu'a ga ma'auratan

Umahi ya bayyana yadda Ubangiji ke gudanar da lamuransa cikin hikima inda ya bayyana alakarsa da gwamna Nwifuru tsawon shekaru.

Ya ce Allah ne ya haɗa su cikin nufinsa, kuma wannan aure ya ƙara haɗa iyalansu bayan shekaru fiye da 18 da suke da zumunci mai ƙarfi.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya tara malaman Musulunci a Zamfara, ya nemi alfarmarsu

Umahi ya taya su murna, yana addu’ar Allah ya cika musu burinsu da zaman lafiya, albarka da soyayya.

Yan siyasa sun halarci auren yan uwan Umahi da Nwifuru
Hotunan da aka dauka a auren kanin Umahi da kanwar Gwamna Nwifuru. Hoto: Senator Engineer David Nweze Umahi, CON.
Source: Facebook

Umahi ya fadi muhimmancin auren gare su

Ministan ya ce wannan aure ya zama hujjar cewa dangantaka ta gaskiya da amana tana iya kawo haɗin kai tsakanin iyalai da al’umma baki ɗaya.

Ya kara da cewa:

Lallai Allah yana da nasa hanyoyin yin abubuwa. Dangantakata da Gwamna Francis Nwifuru ta fara ne sama da shekaru18 da suka wuce, bisa soyayya, amana da gaskiya, kuma yanzu Allah ya sa wannan zumunci ta gangara ga kannenmu.
Ina taya Silas da Rebecca murna, ina addu’ar Allah ya sa wannan aure nasu ya ci gaba da bunƙasa cikin kauna, zaman lafiya da albarka."

Mahaifin gwamna a Najeriya ya zama Sarki

A baya, kun ji cewa an nada mahaifin Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi sarki a yankin a wani yankin jihar ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2025.

Al'ummar yankin da ke karamar hukumar Izzi sun amince da nadin Eze Ezekiel Nwifuru Nwankpu a matsayin sarkinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta soke amfani da JAMB wajen shiga jami'a? An samu bayanai

Sabon basaraken ya auri mata 19 a rayuwarsa amma yanzu yana rayuwa da mata 17 da tulin ya'ya har 108 ciki har da Gwamna Nwifuru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.