Birne Sarki a Tsarin Musulunci Ya Bar Baya da Kura, Sarakuna Sun Samu Sabani
- Mutuwar Oba Sikiru Kayode Adetona, tsohon Awujale na Ijebuland, ta haifar da rikici tsakanin masu ra’ayin gargajiya da na addini
- Hakan ya biyo bayan an birne marigayin bisa ka’idojin Musulunci maimakon na gargajiya kamar yadda aka saba
- Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya yaba da wannan mataki, yana cewa ya kawo sabon tsari ga sarakunan Yarbawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Mutuwar Sarki Sikiru Kayode Adetona ya haddasa rikici tsakanin manyan sarakunan Yarbawa.
Marigayin kafin rasuwarsa shi ne Awujale na Ijebu, da aka birne shi bisa ka’idojin Musulunci wanda hakan ya haddasa rigima a yankin.

Source: UGC
Birne Sarki ya raba kan sarakunan Yarbawa
Rahoton Vanguard ya ce masu bin addinin gargajiya sun zargi gwamnati da keta dokokin al’ada, suna cewa an tauye hakkinsu na gudanar da bukukuwan da ake yi wa sarakuna bayan mutuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, sun yi barazanar daukar mataki a kotu don kare al’adunsu musamman yayin birne sarakuna a yankin.
Sai dai Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya ce abin da aka yi ga marigayi Sikiru Adetona “nasara ce ga sarakuna da al’umma.”
Ya ce, daga yanzu, duk Sarkin da yake son a raba shi da gawarsa ko a yi masa zalunci bayan mutuwa zai iya zaɓar hanyar birne shi da kansa.
Ya yaba da marigayin Awujale da gwamnati bisa tsayin daka wajen bin dokar da ta ba Sarki damar zabar irin jana'izarsa.

Source: Twitter
Sarakuna sun soki birne Sarki bisa tsarin Musulunci
Amma wasu sarakuna kamar Deji na Akure, Olowo na Owo, da masu bin al’adun Isese sun nuna rashin amincewa, cewar Punch.
Sun ce, Sarki da ya amshi rawani dole ne ya zauna bisa al’adar gargajiya, ba wai ya bari wani addini ya mamaye masarautarsa ba.
Suka ce cire al’adun gargajiya daga jana’izar sarakuna “wulakanci ne ga al'adun Yarbawa,” kuma idan Sarki bai shirya bin tsarin gargajiya ba, ya fi dacewa ya ki zama Sarki tun da farko.
Martanin mabiya addinin gargajiya kan lamarin
A cewar Araba na Osogbo, Cif Ifayemi Elebuibon ya ce a al’adar Yarbawa, idan mutum zai zama sarki na gargajiya sai ya bi wasu tsare-tsare domin buɗe hanya tsakaninsa da kakanninsa.
Haka nan, idan ya rasu, ana yin irin wannan tsarin na Oro don nuna ƙarshen mulkinsa da cikar wa'adinsa bayan hawa karaga.
Kowane yanki yana da nasa hanya ta birne matattu, a al’adar Yarbawa, tun kafin zuwan addinan Turawa, akwai hanyoyi na musamman da ake birne mutane daban-daban.
Sarkin Ijebu ya kwanta dama
A baya, mun ba ku labarin cewa a ranar da Muhammadu Buhari ya rasu, Najeriya ta sake shiga alhini yayin da Sarkin Ijebu, Sikiru Adetona, ya rasu yana da shekaru 91.
Gwamna Dapo Abiodun wanda ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya marigayin ya taimaka wajen gina kasar Ijebu da ma jihar Ogun.
Oba Adetona ya hau sarauta a 1960, ya yi mulki tsawon shekaru 65, kuma ya inganta kasarta ta fuskar ilimi, lafiya da sauran su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


