'Yan Ta'addan Boko Haram, ISWAP Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Ta'addan Boko Haram, ISWAP Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin sama da tsaro sun fuskanci harin kwanton bauna daga wajen 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP
  • 'Yan ta'addan sun shammaci sojojin ne lokacin da suka fita aiki a karamar hukumar hukuma Bama a jihar Borno
  • Fafatawar da aka yi tsakanin dakarun sojoji da 'yan ta'addan ta jawo an samu asarar rayuka masu yawa daga bangarorin guda biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da dama da ake zargin mambobin Boko Haram da ISWAP ne a jihar Borno.

Sojojin sun samu nasarar ne a wani artabu da ya auku yayin da su ke gudanar da aikin share sansanonin ‘yan ta’adda a yankin Bama-Kashimri, karamar hukumar Bama, a jihar Borno.

Sojoji sun yi artabu da 'yan Boko Haram a Borno
Sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Jumma'a, 17 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida

Sojoji sun yi arangama da 'yan Boko Haram

Wata majiya mai tushe daga bangaren sojoji ta bayyana cewa dakarun sun fuskanci harin kwanton-bauna ne a lokacin da suke aikin kakkabe yankin Kashimri.

“Dakarun Operation Hadin Kai sun mayar da martani cikin gaggawa tare da karfi, inda suka kashe ‘yan ta’adda fiye da 30, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbi."

- Wata majiya

Sai dai, majiyar ta bayyana cewa, jami’in da ya jagoranci aikin (ba a bayyana sunansa ba), tare da wasu sojoji, mambobi biyu na CJTF, da 'yan sa-kai biyu, sun rasa rayukansu a fafatawar.

“Eh, sojojinmu sun gamu da kwanton bauna daga Boko Haram a kan hanyar Bama–Kashimri ranar Jumma’a yayin da suke aikin share sansanin 'yan ta'adda."
"Sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama, sai dai mun yi rashi na jami’anmu da wasu daga cikin masu taimakawa."

- Wata majiya

Kara karanta wannan

Ba sauki: Sojojin sama sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Neja

Sojoji sun fafata da 'yan Boko Haram
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji za su ci gaba da fatattakar 'yan ta'adda

Duk da asarar, majiyar ta tabbatar da cewa dakarun sun ci gaba da kasancewa cikin kwarin gwiwa, tare da ci gaba da ayyukan kakkabe sauran yankuna don hana ‘yan ta’adda motsi da kafa sansani.

“Sojojinmu suna ci gaba da matsa lamba a dukkan fannoni don hana ‘yan ta’adda samun sarari ko motsi a yankin Arewa maso Gabas,”

- Wata majiya

Sojoji sun yi bajinta

Abdullahi Sani ya shaidawa Legit Hausa cewa dakarun sojoji sun nuna bajinta sosai wajen yaki da 'yan ta'addan.

"Gaskiya wannan nasarar abin a yaba ce. Dakarun sojoji suna matukar kokari wajen yaki da 'yan ta'adda."
"Muna fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara kan wadannan miyagun mutanen."

- Abdullahi Sani

Karanta wasu labaran kan sojoji

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su

Sojoji sun cafke hatsabibin dan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani hatsabibin dan ta'adda da aka dade ana nema ruwa a jallo.

Dakarun Operation UDO KA na rundunar sojojin Najeriya, su ne suka kama Ifeanyi Eze, wanda aka fi sani da Gentle De Yahoo, a jihar Imo.

Gentle De Yahoo na daya daga cikin fitattun kwamandojin kungiyar 'yan aware ta ta IPOB/ESN, wadda gwamnatin tarayya ta haramta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng