Majalisa Ta Yi Karin Haske kan Bukatar Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026

Majalisa Ta Yi Karin Haske kan Bukatar Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026

  • Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe ya yi magana kan neman dawo da zabubbukan 2027 zuwa 2026
  • Ya bayyana cewa bukatar tana matakin sauraron ra’ayoyin jama’a ne kawai, kuma ba a amince da ita a majalisa ba har yanzu
  • Adebayo Balogun ya ce jama’a da kungiyoyi ne suka nemi a tabbatar da kammala shari’u kafin a rantsar da zababbun shugabanni

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe, Adebayo Balogun, ya bayyana dalilin da yasa aka nemi a yi zabe a watan Nuwamba 2026, maimakon Fabrairu 2027.

Daga cikin dalilan, ya ce akwai samar da isasshen lokaci don kammala karar zabe a kotu kafin a rantsar da sabon shugaban kasa.

Shugaba Bola Tinubu a majalisa
Shugaban Najeriya yana wani bayani a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A hirar da ya yi da Daily Trust, ya ce bukatar tana cikin kudirin gyaran dokar zabe na shekarar 2025, wanda har yanzu yana matakin sauraron ra’ayoyin jama’a.

Kara karanta wannan

An nemi tayar da gobara a matatar Dangote da wasu matsaloli sama da 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Balogun ya ce ba a kai ga yanke matsaya a majalisar ba, domin a yanzu ra’ayoyi ne kawai ake tattarawa kafin a gabatar da rahoto da karatu na uku a majalisar.

Dalilin neman dawo da zabe 2026

Balogun ya bayyana cewa manufar sauya lokacin zaben ita ce a tabbatar da cewa shari’un sakamakon zabe sun kammala kafin ranar rantsar da shugabanni.

Ya ce:

“A baya an ba da tazarar shekara guda domin kammala karar zabe, daga baya aka rage zuwa wata shida.
"Don haka idan ana son rantsar da shugabanni a Mayun 2027, babu makawa sai an yi zabe kafin karshen watan Nuwamban 2026.”
Sabon shugaban INEC
Sabon shugaban INEC, Farfesa Amupitan. Hoto: Plateau State Government
Source: Twitter

Ya kara da cewa wannan bukata ce daga jama’ar kasa da kungiyoyin farar hula, ba daga majalisar ba.

“Jama’a ne suke so a kammala karar zabe kafin a rantsar da gwamnati, don haka dole ne a samu lokaci don yin hakan,”

Kara karanta wannan

Zaben 2019: Yadda Akpabio ya yi karyar an yi masa magudin zabe a gaban Sanatoci

In ji shi.

Martani kan zargin da aka yi wa APC

Da yake mayar da martani kan zargin cewa kudirin yana neman amfani da tsarin don amfanin shugaban kasa da jam’iyya mai mulki, Balogun ya ce wannan batu ba shi da tushe.

Ya yi tambaya da cewa:

“Su waye suke yin wannan ikirari? Su ne irin mutanen da suke son a kammala shari’u kafin rantsarwa. To, ta yaya hakan zai yiwu ba tare da an ware lokaci ba?”

Ra’ayoyin jam’iyyun siyasa da jama’a

Wasu jam’iyyun siyasa sun bayyana cewa dawo da zabe shekarar 2026 ba zai ba su damar shiryawa ba, amma Balogun ya ce wannan ba uzuri ba ne idan dai sun shirya shiga zabe.

Balogun ya shawarci jama’a da su tuntubi wakilan su a majalisa idan suna son goyon bayan wannan gyara lokacin da aka kai shi gaban majalisar don amincewa.

INEC ta ce za a yi adalci a 2027

Kara karanta wannan

'Za a yi sahihin zaben da kowa zai yi yarda da shi a 2027,' Shugaban INEC

A wani labarin, mun kawo muku cewa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya yi magana kan zaben 2027.

Shugaban ya bayyana cewa zai tabbatar da cewa an yi sahihin zabe da har wanda ya fadi zai taya wanda ya lashe murna.

Baya ga haka, ya ce zai tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun kara samun kwarin gwiwa da gamsuwa game da zabukan da za a yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng