Nnamdi Kanu: Amurka Ta Fitar da Gargadi bayan Saka Ranar Zanga Zanga a Najeriya

Nnamdi Kanu: Amurka Ta Fitar da Gargadi bayan Saka Ranar Zanga Zanga a Najeriya

  • Ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar da gargadi kan wata zanga-zangar da za a yi a ranar Litinin, 20 ga Oktoba
  • Zanga-zangar da ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya shirya, na neman a saki shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
  • Amurka ta shawarci ‘yan ƙasarta su guji yankin Eagle Square da wuraren da ake hasashen tarzoma a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan ƙasarsa kan zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 20 ga Oktoba, 2025.

An bayyana cewa zanga-zangar da ɗan takarar shugaban ƙasa a baya kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya shirya, za ta gudana a sassan Abuja.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sowore ya bayyana a shafinsa na X cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana, kuma manufarta ita ce neman a saki shugaban ƙungiyar 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu,

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargadin Amurka kan zanga-zangar Nnamdi Kanu

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a ranar Juma’a, an ce zanga-zangar na iya haifar da matsaloli.

Daga cikin abubuwan da ake fargabar za su faru akwai cunkoson abubuwan hawa, toshe hanyoyi, da yiwuwar rikici tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga.

Ofishin ya umarci ‘yan ƙasar Amurka da ke Abuja da su guji yankin da za a gudanar da zanga-zangar, tare da takaita zirga zirga a cikin birnin a ranar Litinin.

An kuma ba da shawarar cewa yara su zauna gida, sannan ma’aikatan da ke zuwa daga wajen Abuja su guji tafiya zuwa birnin a wannan rana.

Shawarar Amurka ga 'yan kasarta

Ofishin jakadancin Amurka ya ce:

“Dole ne ‘yan ƙasar Amurka su guji wuraren da ake yin zanga-zanga, su guji shiga tarin jama’a, kuma su yi taka tsan-tsan idan suka tsinci kansu a kusa da taron jama'a.”

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin kayar da Paul Biya, ana kone kone a Kamaru kan 'magudin zabe'

An kuma shawarce su da su kasance a fadake, su tabbata wayoyinsu na da caji domin kiran gaggawa idan wani abu ya faru.

Ofishin ya kara da cewa akwai yiwuwar tashe-tashen hankali yayin zanga-zangar, don haka ‘yan ƙasar Amurka su kasance cikin shiri da kulawa sosai.

Dalilin yin zanga zangar Nnamdi Kanu

Zanga-zangar ta samo asali ne daga matsin lamba da ake yi don ganin an saki shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu.

Hukumomin Najeriya sun tsare Nnamdi Kanu tun daga 2021 bayan an dawo da shi daga kasar Kenya.

Kanu yana fuskantar tuhumar ta’addanci a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kuma 'yan ƙungiyar IPOB da magoya bayansa sun dade suna kira da a sake shi.

Amurka ta karyata kisan Kiristoci

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Amurka ta karyata zargin da ake yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Hadimin shugaba Donald Trump ne ya bayyana haka bayan ganawa da Bola Tinubu a ranar Juma'a, 17 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama miji da mata masu safarar makamai ga ƴan ta'adda a jihohin Arewa

Ya bayyana cewa rashin tsaro ya shafi dukkan 'yan kasa kuma 'yan ta'adda sun fi kashe Musulmi a Najeriya a kan Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng