'Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Caji Ofis, Sun Harbe 'Yan Sanda har Lahira a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Caji Ofis, Sun Harbe 'Yan Sanda har Lahira a Kaduna

  • ‘Yan bindiga sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda a garin Zonkwa, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna
  • Jami’ai biyu na rundunar ‘yan sandan sun rasa rayukansu yayin da 'yan bindigar suka bude masu wuta a ranar Jumma’a
  • Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne domin ’yantar da wasu masu laifi da 'yan sanda suka kama a Kachia

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A shiga tashin hankali a garin Zonkwa da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, yayin da 'yan bindiga suka farmaki ofishin 'yan sanda.

An ruwaito cewa, 'yan ta'addan masu tarin yawa sun farmaki ofishin 'yan sandan ne a yanayin ba-zata, inda suka kashe jami'ai biyu nan take.

'Yan sanda sun mutu yayin da 'yan binda suka farmaki caji ofis a Kaduna
Hoton wasu daga cikin motocin sulke da gwamnati ta ba 'yan sanda a Kaduna. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sanda

Kara karanta wannan

APC za ta ci gaba da raunata 'yan adawa, Yilwatda ya fadi manyan ADC da za su koma jam'iyyar

Wannan mummunan lamari, da ya jefa mazauna garin Zonkwa a cikin tashin hankali, ya faru ne a yammacin ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani da abin ya faru kan idonsa, ya shaidawa jaridar cewa, 'yan bindigar sun bude wuta dai dai lokacin da suka shiga ofishin 'yan sandan.

Shi dai wannan ofishin 'yan sandan, yana dan nesa kadan da otel din Kamyim, a Kurmin-Bi Zonkwa.

Majiyar ta yi zargin cewa, 'yan ta'addar sun kai harin ne a wani yunkuri na kubutar da wasu masu laifi da aka kama a garin Kachia kwanan baya.

An kashe jami'an 'yan sanda 2 a Kaduna

Wanda abin ya faru a kan idonsa, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Suna zargin cewa wadanda aka kama din an tsare su ne a ofishin 'yan sanda na Zonkwa.
"Amma, daga baya ne aka fahimci cewa ba a wannan ofishin ne aka tsare masu laifin ba. To sai dai, aikin gama ya gama, don sun yi ta'asa kafin su fahimci hakan."

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar, amma ba ta yi wani karin bayani game da halin da ake ciki ba.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

Wani bidiyo da aka gani, ya nuna irin barnar da 'yan ta'addan suka yi, inda aka ga gawar wasu 'yan sanda kwance a cikin jini.

An ce 'yan bindigar sun farmaki 'yan sandan ne don kubutar da wasu masu laifi a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da ke a shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane sun shiga fargaba a Kaduna

Daga bisani ne aka samu wasu gungun mutane a wurin da abin ya faru, suna tattaunawa kan harin, wanda ya kara fito da matsalar tsaro da ke ta'azzara a kasar.

Sai dai rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya bayan karin jami’an tsaro sun isa wurin.

Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da sanarwa game da lamarin ba.

Mutane a yankin suna bayyana damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke kara tsananta a jihar da ma yankin Arewa maso yamma baki ɗaya.

'Yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga 200 sun kai farmaki garin Babanla, jihar Kwara, inda suka kashe dan sanda tare da kwace bindigarsa.

ASP Adejumo Wasiu ya rasa ransa a harin da 'yan ta'addar suka kai ofishin ‘yan sanda na Babanla, kafin su farmaki kasuwar garin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Bago ya samo hanyar magance 'yan ta'adda

Majiyoyi sun ce 'yan ta'addar sun yi kaca-kaca da ofishin ‘yan sandan, amma ba su samu ƙarin makamai ba saboda jami'ai sun fita aiki da sauran bindigogin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com