Binciken Kwakwaf kan Ikirarin Nuru Khalid Na Cewa Turawa ne Suka Kafa Wahabiyanci

Binciken Kwakwaf kan Ikirarin Nuru Khalid Na Cewa Turawa ne Suka Kafa Wahabiyanci

  • Malamin Musulunci da ke zaune a birnin tarayya Abuja, Muhammad Nuru Khalid ya yi ikirarin cewa Turawa ne suka kafa wahabiyanci
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar da wani wa'azi, kuma ya kalubalanci mutane su duba tarihi domin tabbatar da hakan
  • A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bincike kan maganar malamin tare da duba tarihin mutumin da ya ce ya jagoranci kafa wahabiyanci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Maganar Sheikh Muhammad Nuru Khalid kan cewa wani bature, Thomas Edward Lawrence ne ya jagoranci kafa Wahabiyanci ta jawo ce-ce-ku-ce.

A kan haka ne lokacin Hausa ta yi nazari kan tarihin Thomas Edward Lawrence da Muhammad bin Abdulwahad domin nazarin maganar Nuru Khalid.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Malam Muhammad Nuru Khalid
Malam Nuru Khalid yana huduba a masallaci. Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Source: Facebook

Malam Nuru Khalid ta yi maganar ne yayin wani wa'azi kamar yadda ya wallafa bidiyon a shafisa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Nuru Khalid kan Wahabiyanci

A wa'azin da ya yi, Malam Nuru Khalid ya yi ikirarin cewa an kafa Wahabiyanci ne domin a raba kan Musulmi.

Ya ce:

"Gwamnatin Ingila, Birtaniya su suka kirkiri Wahabiyanci, an yi amfani da Lawrence of Arabia wajen yin haka.
"Ku je ku karanto tarihi ku ce mana ba haka ba ne."

Shakka babu ana alakanta Lawrence of Arabia da raba kan kasashen Musulmi, sai dai mun yi bincike game da zargin shi ya kafa Wahabiyanci.

Yaushe aka haifi Lawrence of Arabia?

Rahoton BBC ya nuna cewa an haifi Thomas Edward Lawrence da ake cewa Lawrence of Arabia ne a ranar 16 ga Agusta, 1888 a Arewacin Wales.

Lawrence ya yi karatu a Jami’ar Oxford, sannan a shekara ta 1909 ya ziyarci ƙasar Siriya da Falasɗinu.

Bayan shekara guda, ya shiga aikin tono kayan tarihi a Siriya, inda ya zauna daga 1911 zuwa 1914, yana koyon harshen Larabci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

Lawrence ya bar aikin rundunar sojojin sama (RAF) a watan Fabrairu, 1935, kuma ya rasu a ranar 19 ga Mayu na 1935 din bayan haɗarin babur kamar yadda shafin Britannica ya tabbatar.

Waye Muhammad bin Abdulwahhab?

Mawallafin littafin The Life, Teachings and Influence of Muhammad ibn Abdulwahhab, Jamaaluddin Zarabozo ya ce an haifi Muhammad bn Abdulwahhab ne a shekarar 1703 a garin Uyaynah.

Saboda 'Abdulwahhab' ne sunan mahaifin malamin wasu ke jingina koyarwar da ya yi da Wahabiyanci.

Wani rahoto da shafin Britannica ya wallafa ya nuna cewa Muhammad bin Abdulwahhab ya rasu a shekarar 1792.

Nazari kan ikirarin Nuru Khalid

A maganar da Nuru Khalid ya yi, ya ce Birtaniya ta yi amfani da Lawrence wajen kafa Wahabiyanci da Muhammad bin Abdulwahhab ya jagoranta.

Lura da cewa Muhammad bin Abdulwahhab ya rasu a shekarar 1792, shi kuma Lawrence an haife shi a 1888 ba zai yiwu a ce sun yi zamani tare ba.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Malam Nuru Khalid yana wani wa'azi. Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Source: Facebook

Maganar Nuru Khalid gaskiya ce?

Idan aka lura, za a ga cewa tsakanin mutuwar Muhammad bin Abdulwahhab da haihuwar Lawrence of Arabia akwai tazarar shekara 96.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

Hakan ya nuna cewa ikirarin Malam Nuru Khalid na cewa an yi amfani Lawrence wajen kafa Wahabiyanci da Muhammad bin Abdulwahhab ya jagoranta ba gaskiya be ne.

A karshe dai an tabbatar da cewa akwai kuskure a maganganun malamin da aka fi sani da Digital Imam.

Malaman Arewa sun yi taro a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin Musulunci a Arewacin Najeriya sun yi taro a jihar Kaduna.

Taron malaman ya mayar da hankali kan manyan matsalolin da suka shafi Arewacin Najeriya kamar tsaro da sauransu.

Manyan 'yan siyasa da sarakunan gargajiya daga Arewacin Najeriya sun halarci taron tare da nuna goyon baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng