Ta Tabbata, Sojojin Najeriya Sun Kama Hatsabibin Ɗan Ta'adda da Aka Jima Ana Nema

Ta Tabbata, Sojojin Najeriya Sun Kama Hatsabibin Ɗan Ta'adda da Aka Jima Ana Nema

  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kama Ifeanyi Eze, babban kwamandan ‘yan ta’addaN IPOB/ESN a jihar Imo
  • An kuma kama wata mata da ke taimaka wa IPOB a jigilar kayayyaki tare da gano ‘ya’yan wani shugaban kungiyar da aka haramta
  • Sojoji sun kwace makamai, harsasai da mota daga hannun wadanda ake zargi yayin samame a jihohin Imo, Abia da Ebonyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun samu nasarar cafke daya daga cikin fitattun kwamandojin kungiyar IPOB/ESN.

Hedikwatar ta ce dakarun Operation UDO KA na rundunar sojin Najeriya, su ne suka kama Ifeanyi Eze, wanda aka fi sani da Gentle De Yahoo, a jihar Imo.

Sojojin Najeriya sun kama wani kwamandan 'yan IPOB a jihar Imo
Dakarun sojojin Najeriya suna atisaye a wani yankin Najeriya. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kama hatsabibin dan ta'adda

Daraktan yada labarai na tsaron kasa, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, inji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta soke amfani da JAMB wajen shiga jami'a? An samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Markus ya ce an kama Eze ne tsakanin 8 zuwa 13 ga watan Oktoba, 2025, a wani samame da dakarun suka kai a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A cewar Markus, Eze yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo, tare da wasu takwas da ke ta’addanci a Kudu.

Ya shaidawa menama labarai cewa Eze da tawagarsa na gudanar da ayyuka a Owerri ta Yamma da yankin Mbaitoli a jihar Imo, da kuma Izzi da Ohaukwu a jihar Ebonyi.

An kama wata mata mai taimakawa IPOB

Manjo Janar Markus ya ce dakarun sun kuma kama wata mata da ake zargi da taimakawa IPOB/ESN a bangaren sufuri da kayayyakin yaki a Umunneochi, jihar Abia.

A yayin wannan samame, an gano ’ya’ya uku na wani shugaban kungiyar da ake nema, Maduabuchi Nwankwo, wanda aka fi sani da Emergency, a hannunta.

“Binciken farko ya tabbatar da cewa wannan mace ‘yar uwar shugaban kungiyar ce,”

Kara karanta wannan

Jos, Gombe da wasu birane da ake sayar da litar fetur N1000, an samu sauki a Kano

- in ji Manjo Janar Markus.

A cewar rundunar, dakarun sun kwace makamai, harsasai, da mota daga hannun wadanda aka kama yayin wannan aiki.

An ce an kama wata mata mai taimakawa 'yan ta'addan IPOB a Imo.
Taswirar jihar Imo da ke a Kudu maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tarihin dan ta'addan da sojoji suka kama

Ifeanyi Eze, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai fafutukar kafa kasar Biafra, yana da hannu a hare-haren da suka addabi yankin Okigwe a Imo.

Ana zargin sa da kisan wasu daga cikin mayakansa bayan sabani a cikin kungiyarsu, inji rahoton TVC News.

Eze shi ne kwamandan rundunar BLA, wata rundunar ce da Simon Ekpa, jagoran ɓangaren Autopilot na IPOB, ya kafa.

A watan Satumba, an ruwaito cewa Eze da tawagarsa sun fada hannun dakarun soja a Aku-Ihube, karamar hukumar Okigwe. Sai dai yanzu hedikwatar tsaro ta tabbatar da cewa an kama shi da ransa kuma yana hannun jami’an tsaro.

Gwamna ya kawo batun sakin Kanu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu, ya bayyana cewa akwai bukatar tattauna batun shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ta fuskar siyasa.

Kara karanta wannan

Tofa: Peter Obi ya maka sanannen lauya a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan 1.5

Gwamnan wanda ya koma jam'iyyar APC daga PDP ya ce lokaci ya yi da za a tsahirta da batun shari'ar Kanu, a warware matsalar ta fuskar siyasa don ci gaban Kudu.

Peter Mbah ya bayyana cewa, ya gana da Shugaba Bola Tinubu kuma ya bijiro masa da bukatar sakin jagoran na kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com