An Kama Wanda Ake Zargi Da Ɗaukan Nauyin Ƴan IPOB/ESN, Da Wasu Mutum 25 a Otel

An Kama Wanda Ake Zargi Da Ɗaukan Nauyin Ƴan IPOB/ESN, Da Wasu Mutum 25 a Otel

  • Yan sanda a jihar Imo sun cafke wani mutum da ake zargi da daukan nauyin yan IPOB
  • Boniface Okeke ya amsa cewa ya bawa IPOB/ESN a kalla N10m a lokacin yana kasan waje
  • Yan sandan sun kuma kama wasu mutane 25 da ake zargin yan IPOB ne a wani Otel a Orlu

Yan sandan jihar Imo sun ce sun kama wani mutum da aka ce ya amsa cewa yana daga cikin masu daukan nauyin ayyukan kungiyar masu son kafa Biafara wato IPOB da ESN, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kyautata zaton Boniface Okeke ya bada gudunmawar a kalla Naira miliyan 10 ga kungiyar IPOB, a cewar mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abbatam cikin wata sanarwa da ya fitar.

An Kama Wanda Ake Zargi Da Ɗaukan Nauyin Ƴan IPOB/ESN, Da Wasu Mutum 25 a Otel
Wasu da ake zargin yan kungiyar IPOB ne da aka kama a Otel. Hoto: The Nation
Asali: UGC

The Nation ta ruwaito cewa nn kama shi ne a garin Obor autonomous da ke karamar hukumar Orlu na jihar kan zarginsa da alaka da ta'addanci da kai wa jami'an tsaro hari da ma farar hula.

Kara karanta wannan

An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka

Yan sanda da dama sun mutu an kuma kona caji ofis da dama sakamakon harin.

Ya ce:

"Da ake masa tambayoyi, ya amsa cewa yana daga cikin masu daukan nauyin IPOB/ESN a jihar inda ya bada gudunmawar a kalla Naira miliyan 10 yayin da ya kasar waje.
"Ya taimakawa yan sanda wurin kama wasu mambobin kungiyar da kuma rushe sansaninsu a jihar."

Yan sanda sun kama wasu yan IPOB 25 a Otel

Har wa yau, yan sandan sun kuma kama wasu mutane da ake zargi yan IPOB ne, ciki har da mata bakwai a wani otel a Orlu.

Kwamishinan yan sandan jihar Imo Abutu Yaro ya ce wadanda aka kama ana zarginsu ne da hannu wurin aikata ta'addanci kan faran hula da jami'an tsaro.

Shugaban yan sandan ya ce an kama su ne da taimakon wani Emmanuel Nnaji, dan asalin garin Awala a karamar hukumar Ideato na Kudu a Imo wanda aka kama bayan harin da aka kai a ofishin yan sanda na Omuma da Njaba.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

Ya kuma ce an samu makamai hannun su kamar bindiga AK 47 biyu da harsashi, bindiga kirar double barrel, double barrel ta Nigeria, Pistol da harsahinta, layyu da guru, buhuna biyu da wani ganye da ake zargin wiwi ne, tuta da unifom na Biafra da wasu kayayakin masu dauke da tambarin Biafra.

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164