‘Ku Rubuta Wasiyya ga Iyalanku’: Gwamna ga Masu Neman Raba Shi da Mulkinsa
- Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya gargadi ‘yan siyasa masu shirin yin magudi a zaben gwamna na 2027
- Otti ya ce nufin Allah da ra’ayin jama’ar jihar Abia ne kawai zai tantance sakamakon zabe, ba makirci ko dabarun siyasa ba
- Gwamnan ya bayyana cewa duk wanda ya nemi sauya zabin jama’a zai gamu da sakamakon da ya dace da shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya yi gargaɗi mai tsanani ga wasu ‘yan siyasa da ke da niyyar yin magudi a zaben jihar.
Gwamna Alex Otti ya ce akwai wasu da ke maganganu cewa za su kwace jihar a zaben shekarar 2027 da ake tunkara karfi da yaji.

Source: Twitter
Gwamna ya gargadi masu shirin magudin zabe
Rahoton Channels TV ya ce Gwamna Otti Otti ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis 16 ga watan Oktoban 2025.
A taron da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Umuahia, Otti ya ce duk mai shirin magudin zabe ya rubuta wasiyya kafin ya aikata.
Gwaman Otti ya ce:
“Idan suna da niyyar rubuta sakamakon zabe da suka ga dama, to su fara rubuta wasiyyar su tun kafin lokacin.”
Gwamnan ya bayyana cewa nufin Allah da kuma ra’ayin jama’ar jihar Abia ne kawai za su yanke hukunci kan wanda zai lashe zaben mai zuwa, ba makirci ko amfani da karfin siyasa ba.
“Na ji wasu suna cewa dole sai sun kwace jihar nan, suna shirye su rubuta sakamako, to, shawarar da nake da ita a gare su ita ce su rubuta wani abu kafin nan – wasiyyar su.”
- Alex Otti

Source: Facebook
Abia: Abin da masu magudi za su fuskanta
Gwamnan ya kara da cewa ba shi da matsala da duk wanda zai fito takara, amma duk wanda ya nemi karkatar da zabin jama’a zai fuskanci sakamako mai tsanani.
Ya kara da cewa:
“Zabe dimukradiyya ce, kowa na da damar tsayawa takara. Amma wadanda suke shirin yin magudi, su shirya su fuskanci abin da zai biyo baya.”
Wannan gargadin ya zo ne yayin da ake ganin an fara shirye-shiryen siyasa da tattaunawa kan zaben a jihar Abia tun kafin zaben 2027, cewar rahoton Leadership.
Gwamna Otti, wanda ya kawo ƙarshen mulkin PDP da ya dauki fiye da shekaru 20 a jihar da nasararsa a zaben 2023, ya jaddada cewa gwamnatinsa tana maida hankali kan ingantaccen mulki kuma ba za ta bari rigimar siyasa ta raba mata hankali ba.
Gwamna ya nemi diyya bayan kiransa barawo
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya nuna damuwa kan yada wasu bayanai a manhajar Facebook da ke zubar masa da mutunci.
Alex Otti ya nemi diyya ta Naira biliyan 100 daga tsohon kwamishina, Eze Chikamnayo kan wallafe-wallafen bata suna da suka taba kimarsa.
Lauyan gwamnan ya ce rubuce-rubucen suna nufin nuna kiyayya da ɓata martabar Otti, wanda ya ce ba a taba tuhumarsa a kotu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


