NNPP Ta Wanke Tinubu daga Zargin Tursasawa 'Yan Adawa Sauya Sheka zuwa APC
- Jagora a jam'iyyar adawa ta NNPP, Dr Boniface Aniebonam ya ce son rai da kokarin cimma manufar siyasa ke jawo sauya sheka da ake gani yanzu
- Sai dai ya jaddada cewa shiga kowace jam’iyya a Najeriya 'yanci ne na kowa, kuma APC ko Shugaba Bola Tinubu ba su yi wa kowa dole ba
- Aniebonam ya yi kira ga jama’a su fahimci siyasar Najeriya, sannan su zabi wanda zai kai su, su ci a babban zabe da ke kara karatowa a 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jagora kuma wanda suka kafa NNPP, Dr. Boniface Aniebonam, ya yi magana a kan sauya shekar gwamnoni da manyan yan adawa zuwa APC.
Ya bayyana cewa babu wani Gwamna ko Sanata da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tilasta wa shiga jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan
Diri: Jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamnan da ya fice daga PDP, ta bayyana dalili

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Boniface Aniebnamu ya ce duk wanda ya sauya jam’iyya ya yi hakan ne saboda ra’ayi na kansa ba wai an tilasta masa ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigo a NNPP ya kare gwamnatin APC
Punch ta wallafa cewa Boniface Aniebonam ya kara da cewa, duk da yawan canja jam’iyyun zuwa APC, hakan ba ya nufin akwai barazanar shiga tsarin jam’iyyar siyasa daya a Najeriya.
Ya kara da cewa:
“Muna da jam’iyyu 18 da aka amince da su a Najeriya. Ko dukkan gwamnonin PDP su koma APC, hakan ba zai canza tsarin jam’iyyu da muka kafa ba.”
Aniebonam ya tunatar cewa Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba zai hana kowa shiga APC ba idan ya ga hakan za ta fishshe shi.
Jagoran NNPP ya shawarci ‘yan Najeriya
Mista Boniface Aniebonam ya shawarci jama’a da su fahimci tsarin siyasa, kuma su zama masu yin nazari da kuma zaɓar abin da ya fi dacewa a nan gaba.

Source: Twitter
Ya kuma roƙi hukumar EFCC da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci su duba jihar da ake zargin gwamnonin da wawashe dukiyar jama’a domin daukar mataki.
Ya bada shawara ga gwamnatin tarayya da hukumomin shari’a da su mayar da hankali wajen kirkiro manufofin da za su amfani al’umma.
Dr Boniface Aniebonam ya kuma jaddada cewa jam’iyyar NNPP ta ke ga duk wanda ke ganin dacewar ya shigo cikinta domin a taimaki jama’a.
NNPP ta nemi afuwar Tinubu
A baya, mun wallafa cewa tsagin NNPP ta nemi gafarar Shugaban kasa, Bola Tinubu da APC kan wasu kalaman cin fuska da alke zargin Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi masu.
Tsagin jam'iyyar da ya ke kokarin raba kan shi da NNPP ta kasa ya bayyana cewa Kwankwaso ba ya cikin NNPP domin tuni aka sallame shi, don haka kalamansa ba matsayarta ba ce.
A wata sanarwa da Dr Oginni Olaposi, mai magana da yawun tsagin NNPP, ya fitar a Legas ya bayyana cewa Kwankwaso ba ya wakiltar NNPP, saboda haka ra'ayinsa ya fada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

