Kwarton da Miji Ya Lakadawa Duka Ya Mutu kan Shiga wajen Matarsa da Dare
- Wani mutum mai shekara 30 ya mutu bayan da wani miji ya lakada masa duka saboda zargin neman matarsa a karamar hukumar Ningi
- ’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar wanda abin ya rutsa da shi bayan an garzaya da shi asibitin Ningi, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa
- A wani lamari na dabam, ’yan sanda sun ceto mutane uku da aka sace tare da kama mutane shida da ake zargi a karamar hukumar Toro
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Wani mutum mai suna Sanusi Tinau, mai shekara 30, ya rasa ransa a Lumbu, karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi kan zargin kwartanci.
Sanusi Tinau ya rasu ne bayan da mijin wata mata ya lakada masa duka saboda zargin neman matarsa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:09 na daren Juma’a, lokacin da Sanusi ya je gidan wani mutumi da ake zargin ya yi yunkurin lalata da matarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa mijin ya farka daga barci, ya afkawa Sanusi, yana dukansa har sai da ya suma, kafin ya tsere daga wurin.
Miji ya kashe kwarto a jihar Bauchi
Jami’an ’yan sanda da ke Ningi sun isa wurin da abin ya faru cikin gaggawa, kuma nan take suka garzaya da Sanusi zuwa asibitin gwamnati.
Likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar Sanusi bayan isarsu, yayin da aka tabbatar da cewa wanda ake zargi ya tsere tun kafin zuwan jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ’yan sanda ya bayyana cewa an fara bincike domin gano inda wanda ake zargi yake domin a gurfanar da shi a kotu.
Ya kara da cewa rundunar ba za ta lamunci daukar doka a hannu ba, kuma za ta tabbatar da cewa an samu cikakken bincike kan lamarin.
’Yan sanda sun ceto mutane 3 a Bauchi
A wani lamari na dabam da ya faru a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, ’yan sanda sun samu nasarar ceto mutane uku da wasu ’yan bindiga suka sace daga kauyen Euga.
An bayyana sunayen wadanda aka sace da cewa su ne Idi Umar, Idi Lawan da Musa Lawal, inda aka kai rahoton sace su da misalin karfe 12:01 na dare a ranar 29, Satumba, 2025.
Bayan samun rahoto, rundunar ’yan sanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na yankin da masu gadin gari suka bi sahun masu garkuwa da mutanen har zuwa wajen kauyen.

Source: Facebook
An gudanar da aikin ceto cikin kwarewa, wanda ya kai ga kubutar da mutanen uku ba tare da wani rauni ba, tare da cafke mutane shida da ake zargi da hannu a lamarin.
Sunayen wadanda aka kama
Rundunar 'yan sandan jihar ta wallafa sunayen wadanda aka kama a shafinta na Facebook kamar haka:
- Abubakar Usman
- Adamu Alo
- Abubakar Aliyu
- Umar Habu
- Abubakar Mamman Abubakar
- Shehu Sambo
Sojoji za su yaki Wulowulo a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa za ta yaki kungiyar 'yan ta'addan Wulowulo da ta bullo.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ne ya bayyana cewa kungiyar ta bayyana a Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Rundunar tsaron ta ce ta sanya kungiyar cikin wacce za a rika sa ido a kanta domin murkushe ta da sauran ire-irensu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

