Gwamnatin Kebbi Ta Jawo Kamfanin Kasar China domin Taya Ta Yaki da Lakurawa

Gwamnatin Kebbi Ta Jawo Kamfanin Kasar China domin Taya Ta Yaki da Lakurawa

  • Gwamnatin Jihar Kebbi ta kulla yarjejeniya da kamfanin tsaro na kasar Sin, Gsafety, domin yakar 'yan bindiga da kungiyar Lakurawa
  • Kamfanin zai samar da fasahar zamani ta leken asiri da tattara bayanan sirri don gano ayyukan miyagu a sassa daban-daban na jihar
  • Za su hada kai da jami’an tsaro da yankunan da lamarin ya fi kamari don karfafa kokarin gwamnatin tarayya na kawo tsaro a Kebbi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da wani sabon shiri na hadin gwiwa da wani kamfanin tsaro na kasar Sin mai suna Gsafety.

Ta bayyana cewa ta jawo kamfanin ne domin yaki da matsalar 'yan bindiga da kungiyar Lakurawa da ke addabar wasu sassan jihar.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

Gwamnatin Kebbi ta nemi taimakon kamfanin Sin a kan tsaro
Hoton Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Nasir Idris Kwauron Gandu
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Shugaban kamfanin Gsafety a Najeriya, Ahmed Sale Jnr, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin China zai yi aiki a Kebbi

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ahmed Sale ya ce kamfaninsu na aiki a kasashe fiye da 36 kuma yana da kwarewa a fannin leken asiri na zaman.

Kamfanin Gsafety za ta taimaka wa jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kara da cewa su kan yi amfani da na'urorin zamani wajen tattara bayanai da shawo kan barazanar tsaro.

A kalamansa:

“Za mu fara amfani da manyan fasahohin zamani ta hanyar tattara bayanai masu muhimmanci da suka shafi ayyukan 'yan bindiga da kungiyar Lakurawa”

Gsafety zai hada kai da jami’an tsaro na matakin ƙasa da yankunan da lamarin ya fi tsananta domin karfafa kokarin gwamnatin tarayya wajen dakile ‘yan ta’adda.

Ana kokarin magance rashin tsaro a kasa

Ahmed Sale ya bayyana cewa ana samun ci gaba a kokarin yaki da rashin tsaro a Najeriya, amma rashin fasahar zamanina daga cikin kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya dura China, ya gana da kamfanoni domin kawo cigaba Kano

Ya ce;

“Wannan shi ne abin da muka zo mu kawo a Jihar Kebbi, kamar yadda muka yi a wasu kasashe. Hedikwatar mu na birnin Beijing, a kasar Sin.”

Ya kuma bayyana cewa fasahar da za su gabatar za ta taimaka wajen tantance barazanar tsaro cikin sauri da kuma sanar da jami’an tsaro matakan da ya dace su dauka.

Ahmed Sale ya tabbatar da cewa kamfaninsu zai bai wa gwamnatin kasar nan gudunmawar da ake bukata wajen kawar da matsalar tsaro da ta addabi jihar Kebbi.

Gwamnati ta yi magana kan hari a Kebbi

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo a wasu gidajen rediyo da kafofin sada zumunta na harin 'yan bindiga ba gaskiya ba ne.

Sanarwar da Sakataren gwamnati, Ahmed ya fitar da sanarwa da cewa har yanzu babu wani hari da 'yan bindiga su ka kai hari, kuma lamarin da aka yada ya faru a Rijau, jihar Neja, ba a Kebbi ba.

Kara karanta wannan

"Akwai matsaloli': Amupitan ya fadi shirinsa kan amfani da BVAS a zabukan Najeriya

Gwamnatin jihar ta Kebbi ta jaddada roko ga jama'a da su bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya don tabbatar da cewa ana ci gaba da kare rayukan mazauna garin yadda ya kamata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng