Gwamna Dauda Lawal Ya Tara Malaman Musulunci a Zamfara, Ya Nemi Alfarmarsu

Gwamna Dauda Lawal Ya Tara Malaman Musulunci a Zamfara, Ya Nemi Alfarmarsu

  • Gwamna Dauda Lawal ya gana da kungiyar malaman addinin Musulunci a gidan gwamnatin jihar Zamfara a jiya Alhamis
  • Dr. Dauda Lawal Dare ya bukaci ƙara yawan addu’o’i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar baki daya
  • Ya jaddada cewa gwamnati ta samu ci gaba wajen yaki da ‘yan bindiga amma za ta ci gaba da aiki har sai an samu zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya nemi alfarmar kungiyar malaman addinin Musulunci a jihar.

Gwamnan ya yi kira ga majalisar malaman ta Zamfara da su ƙara dagewa da addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Dauda Lawal ya roki malaman Musulunci a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal yayin ganawa da malaman Musulunci a Zamfara. Hoto: Mugira Yusuf.
Source: Facebook

Dauda Lawal ya gana da malaman Musulunci

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta soke amfani da JAMB wajen shiga jami'a? An samu bayanai

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Sulaiman Bala Idris ya tabbatar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis 16 ga watan Oktobar 2025 yayin wani taro da ya yi da mambobin Majalisar Ulama.

An gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Gusau karkashin jagorancin Sheikh Umar Kanoma.

Taron ya tattauna kan hanyoyin warware matsalolin ci gaban jihar da kuma yadda za a ƙarfafa wa’azi domin canza tunanin jama’a wajen tallafawa shirye-shiryen gwamnatin jihar.

Gwamna Lawal ya bayyana cewa malamai suna da muhimmiyar rawa wajen gina zaman lafiya, haɗin kai da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin jama’a.

Sanarwar ta ce:

“Malamai suna taka muhimmiyar rawa a duk abin da muke yi a Zamfara, domin suna kusa da jama’a, kuma mutane suna sauraron su musamman wajen gyara tunani da fahimta."

Kara karanta wannan

Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa

Dauda Lawal ya fadi hanyoyin da suke bi domin dakile ta'addanci
Gwamna Dauda Lawal yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Ta'addanci: Ci gaban da aka samu a Zamfara

Dauda Lawal ya bukaci malaman da su ci gaba da wa’azi kan zaman lafiya, bin doka da haɗin kan al’umma, yana mai cewa irin wannan aiki ne zai taimaka wajen cimma burin da ake nema na wanzar da kwanciyar hankali a jihar.

“Mun samu gagarumin ci gaba a yaki da ‘yan bindiga, amma ba mu kai matsayin da muke so ba tukuna. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun dawo da cikakken zaman lafiya a jihar Zamfara. Wannan aiki ne na kowa da kowa, dole mu hada kai mu yi shi tare."

Kara karanta wannan

Malamin addini ya kalli gwamna ido da ido, ya caccake shi a zaman makoki

- Cewar Dauda Lawal

Taron ya kuma tattauna yadda malamai za su ci gaba da tallafawa shirin gwamnatin jihar ta hanyar fadakarwa da inganta fahimtar jama’a kan manufofin ci gaba.

Dauda Lawal ya roki Allah kan ta'addanci

A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda inda ya yi Allah wadai da kisan.

Dauda Lawal ya ce Allah SWT zai tona asiri ya kuma wulakanta masu daukar nauyin ‘yan bindiga, yana kira ga jama’a da su dage da addu’a.

Ya yi alkawarin inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki da ruwa a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.