Ta Tashi: Ganduje da Ƴaƴansa Sun Shiga Uku, Gwamnatin Kano Ta Maka Su a Kotu

Ta Tashi: Ganduje da Ƴaƴansa Sun Shiga Uku, Gwamnatin Kano Ta Maka Su a Kotu

  • A karshe, Gwamnatin Kano ta kai tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, ‘ya’yansa biyu da wasu kotu bisa zargin almundahana
  • Gwamnatin Kano na zargin Ganduje da iyalansa da karkatar da ₦4.49bn daga aikin tsandauri na Dala
  • Rahoton ya ce an yi amfani da kamfanin City Green wajen karkatar da hannun jari 20% na jihar zuwa hannun masu zaman kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ‘ya’yansa biyu da wasu mutane a gaban babbar kotun jihar.

Gwamnatin Kano ta dauki wannan mataki ne kan Ganduje da iyalansa bisa zargin almundahanar N4.4bn wanda ɓangaren tsohon gwamnan ya musanta.

Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da yayansa a kotu
Gwamna Abba Kabir da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

Ganduje: Wadanda ake tuhuma kan badakalar biliyoyi

Rahoton Channels TV ya ce an shigar da karar a ranar 13 ga Oktoba, 2025, inda gwamnati ke neman dawo da 20% hannun jari da kudin da ake zargin an karkatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Taraba ya dauki mataki na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda ake tuhuma sun hada da ‘ya’yan Ganduje: Umar da Muhammad, tsohon mai ba da shawara Abubakar Sahabo Bawuro, da tsohon sakataren hukumar jiragen ruwa Hassan Bello.

Haka kuma ana tuhumar lauya Adamu Aliyu Sanda da tashar tsandauri na Dala da laifukan hada baki, cin amana, da karkatar da dukiyar jama’a.

Gwamnatin Kano ta kuma taso Ganduje a gaba
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin taro a jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Yawan kudin da aka karkatar a tashar tsandauri

Rahoton masu gabatar da kara ya nuna an yi amfani da kamfanin City Green wajen karkatar da hannun jari mallakar jihar zuwa hannun wasu masu zaman kansu.

An kuma ce an karkatar da fiye da ₦4.49bn da aka ware domin gina hanyoyi, samar da wutar lantarki da katanga domin amfanin kamfanoni masu zaman kansu.

Wata majiyar gwamnati ya ce an kashe kudaden ne wajen ayyukan da ke amfanar ‘yan uwa da abokan tsohon gwamna, abin da ya kira cin amana.

Masu gabatar da kara sun ce an yi canjin hannun jarin ba tare da yardar kwamitin gudanarwa ba, tare da amfani da takardun karya.

Kara karanta wannan

'Abba na aiki,' Manyan abubuwan alheri 4 da suka samu jihar Kano a shekarar 2025

Sauran zarge-zarge a tashar tsandauri a Kano

Shaidar da za a gabatar ta hada da biyan ₦750m ta kamfanin Safari Textile da kuma takarda daga gwamnatin tarayya da ke tabbatar da mallakar jihar 20%.

An bai wa Mai Shari’a Yusuf Ubale daga babbar kotu ta biyu shari’ar, inda gwamnatin ta ce za ta dawo da dukiyar jama’a da aka karkatar.

An ce kokarin tuntuɓar tsohon gwamna Ganduje ko lauyoyinsa bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada rahoton domin jin ta bakinsu game da zargin da ake yi musu.

An wanke Ganduje kn zargin badakala

A baya, kun ji cewa tashar tsandaurin Dala ta bayyana cewa babu wani ɗan gidan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da ke da hannun jari a cikinta.

Sakataren tashar, Adamu Sanda, ya ce rahotannin da ake yadawa kan mallakar ‘ya’yan Ganduje ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce ta haddasa su.

Tashar ta bayyana cewa babu wani lokaci a baya da gwamnatin Kano ta mallaki kaso a cikinta ko ta samu wakilci a hukumar gudanarwata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.