Amupitan: Sabon Shugaban INEC Ya Fadi Shirinsa kan Sahihin Zabe a gaban Majalisa

Amupitan: Sabon Shugaban INEC Ya Fadi Shirinsa kan Sahihin Zabe a gaban Majalisa

  • Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan ya halarci zauren majalisa dattawa
  • Farfesa Joash Amupitan ya halarci zauren ne domin tantance shi biyo bayan nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa don jagorantar hukumar
  • Sabon shugaban na INEC ya yi bayani a gaban majalisar kan yadda ya shirya gudanar da sahihin zabe a kasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wanda aka zaba domin zama sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan harkokin zabe.

Farfesa Joash Amupitan, ya yi alkawarin dawo da gaskiya, amana, da cikakken sahihanci cikin harkokin zabe a Najeriya.

Farfesa Amupitan ya sha alwashin yin gaskiya a shugabancin INEC
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan. Hoto: Joash Ojo Amupitan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Farfesa Joash Amupitan ya je majalisar dattawa domin tantance shi a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin cika burin Tinubu, za ta tantance sabon shugaban INEC, Amupitan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Amupitan ya ce a gaban majalisa?

Da yake bayani yayin tantancewar Farfesa Amupitan ya bayyana manufarsa kan harkokin zabe a Najeriya.

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa ya ce manufarsa ita ce a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci har ma wanda ya sha kaye zai taya wanda ya ci nasara murna.

Ya bayyana tsare-tsaren da zai aiwatar idan aka tabbatar da shi, ciki har da kafa kwamitin ladabi da kula da ɗabi’a a cikin hukumar da karfafa gaskiya da bin ka’idar amfani da kuɗaɗen jama’a.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa game da cin hanci da sahihancin zabe, Amupitan ya ce gaskiya da amana sune ginshiƙan jagorancinsa idan aka tabbatar da nadinsa.

Farfesa Amupitan ya kuma bayyana cewa zai yi aiki kafada da kafada da majalisar domin kirkirar hukumar laifuffukan zabe, domin hukunta masu karya dokokin zabe.

Dangane da batun tsaro, Farfesa Amupitan ya bayyana INEC a karkashin jagorancinsa za ta dauki matakan tabbatar da cewa duk wanda ya isa yin zabe ya kada kuri'arsa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta cika baki kan tazarcen Tinubu a 2027

“Batun tsaro babban kalubale ne. Za mu yi aiki tare da hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa babu wani ɗan kasa da za a hana kada kuri’a."
"Za mu bada fifiko wajen samar da kayayyakin sufuri ko da sai mun yi amfani da jirage marasa matuka. Babu wanda za a bari a baya, wannan shi ne alkawarinmu."

- Farfesa Joash Amupitan

Sabon shugaban INEC ya sha alwashi

Farfesa Amupitan ya kuma sha alwashin yin gaskiya wajen gudanar da harkokin kudi na hukumar.

Farfesa Amupitan ya yi bayanai a gaban majalisa
Farfesa Joash Amupitan da aka nada don shugabantar INEC. Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter
“Majalisar nan ta samar da isassun dokoki kan yadda za a sarrafa kuɗin gwamnati. Zan tabbatar da cikakken bin waɗannan dokoki domin a tabbatar da cewa kuɗin gwamnati sun tafi inda ya dace."

- Farfesa Joash Amupitan

NNPP ta fadi matsayarta kan sabon shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi tsokaci kan nadin da aka yi na shugaban hukumar zabe ta INEC.

Jam'iyyar NNPP ta bayyana goyon bayanta kan nadin da Mai girma Bola Tinubu ya yi wa Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Wanda ya assasa jam'iyyar, Boniface Aniebonam ya bayyana cewa Farfesa Amupitan yana da babban aiki a gabansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng