Tofa: Peter Obi Ya Maka Sanannen Lauya a Kotu, Yana Neman Diyyar Naira Biliyan 1.5
- Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, ya kai lauya Deji Adeyanju ƙara a kotu kan furta kalaman ɓata suna
- Tsohon gwamnan yana neman diyyar N1.5bn da kuma rokon afuwa daga Adeyanju kan 'bayanan karya' da ya yi a kansa
- Takardar sammaci ta umarci Adeyanju da ya bayyana a kotu cikin kwanaki 42, domin kare kansa daga zarge-zargen Obi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra – Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya kai lauya kuma mai fafutuka, Deji Adeyanju, ƙara a kotu.
Peter Obi ya shigar da ƙarar ne a babbar kotun jiha ta Anambra da ke da zama a Onitsha, inda yake neman diyyar Naira biliyan 1.5.

Source: Twitter
Rikicin Obi da lauya Deji Adeyanju
Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa, Obi ya zargi Adeyanju da yin rubuce-rubuce na karya da ɓata masa suna a kafafen sada zumunta kamar X, Facebook da Instagram.

Kara karanta wannan
Hana El Rufai taro: Kotu ta umarci 'yan sanda su biya jam'iyyun adawa diyyar N15m
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dai rahoto cewa Deji Adeyanju ya dade yana sukar Peter Obi, inda yake cewa tsohon gwamnan “ba zai taba zama shugaban kasa ba.”
Lauyan ya taba daukar matakin shari'a kan daya daga cikin hadiman Obi, wata Serah Ibrahim, wacce ya ce ta bata sunan matarsa.
Sannan, ya sha yin musayar yawu da magoya bayan Peter Obi, wadanda aka fi sani da 'yan Obidents, kan kalaman da yake furta wa maigidansu,
Obi ya maka lauya Deji a kotu
A watan Agusta, 2025, Peter Obi ya yi barazanar kai Adeyanju ƙara bayan wannan takaddama da ta shafi mataimakiyarsa, Serah Ibrahim.
Sai dai, Deji Adeyanju ya nuna cewa wannan barazanar ta Obi ba komai ba ce sai borin kunya, kuma a shirye yake ya kara da shi a kotu.
A karar da Peter Obi ya shigar, ya ce kalaman Adeyanju sun zubar da mutunci da martabarsa a idon jama’a da duniya.
Takardar sammaci da aka fitar a ranar 3 ga Oktoba ta umurci Adeyanju da ya bayyana a kotu cikin kwanaki 42.
Bukatun da Obi ya gabatarwa kotu
Obi na neman kotu ta umurci Adeyanju da ya wallafa sakon ba da hakuri da neman yafiya a shafukansa na sada zumunta da jaridu uku na ƙasa.
Haka kuma, a wallafa wannan sako a tashoshin talabijin kamar Channels, Arise da TVC don wanke sunansa.
Ya bukaci kotu ta sanya lauyan ya biya shi diyyar a biya shi N1,500,000 a matsayin diyya ta ɓata masa suna da kuma mawuyacin halin da ya jefa shi saboda kalamansa.
Obi ya kuma bukaci kotu ta haramta wa Adeyanju wallafa kalaman da ke zargin sa da tunzara mutane ta fuskar, zama dan damfara ko marar gaskiya.

Source: Twitter
Lauya ya yi martani ga sammacin kotu
A martanin da ya yi a shafinsa na Facebook, Lauya Adeyanju ya tabbatar da samun sammaci daga kotu a ranar Juma’ar da ta gabata.
Lauyan ya ce yana farin ciki da Obi ya kai shi kotu, yana mai cewa shari’ar za ta zama “mai daɗin kallo ga mutane.”
“Zan tabbatar wa kotu cewa Obi ɗan damfara ne kuma mai nuna tsana ga wani bangare na mutane. Ka da ku wani damu, gaskiya za ta yi halinta."
- Deji Adeyanju.
'Ya kamata Atiku ya hakura da takara' - Deji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju, mai rajin kare hakkin dan Adam, ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da yin takara.
A cewar fitaccen lauyan, Atiku na da girman kai, rashin iya mu'amala da mutane da sauran matsalolin da ke tasiri a harkar siyasarsa.
Deji Adeyanju ya tuno yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya ki hada hannu da wasu manyan 'yan siyasa, wadanda a karshe suka koma bayan Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

