Majalisa Ta Fara Binciken Yadda $35m da aka Ware don Gina Matatar Mai Ta Yi Layar Zana
- Majalisar Wakilai ta bayyana takaicin yadda aka ware Dala miliyan 35 domin samar da matatar mai a yankin Neja Delta amma ba labari
- 'Dan majalisar Edo, Billy Osawaru ne ya gabatar da damuwar a zaman da 'yan majalisa su ka yi a ranar Laraba, 15 ga watan Oktoba, 2025
- Ya ce tun bayan da aka fitar da wannan kudi a 2020, babu labarin kudin ko aiki, lamarin da majalisa ta ce ba za ta zuba ido ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da bukatar fara bincike kan yadda $35m da aka ware domin gina wata matatar man fetur bace.
Majalisa ta bayyana damuwa cewa an ware wannan kudi ne domin gina karamin matatar mai a yankin Neja Delta, amma babu wata alama da ke nuna an fara aikin.

Kara karanta wannan
Majalisa na shirin cika burin Tinubu, za ta tantance sabon shugaban INEC, Amupitan

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa majalisa za ta fara binciken ne bayan kudirin da Hon. Billy Osawaru (APC, Edo) ya gabatar a zauren majalisa a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa: Yadda aka so kafa matatar mai
The Nation ta ruwaito cewa Hon. Osawaru ya tunatar da cewa hukumar NCDMB ta fitar da kudin tun a shekarar 2020 domin kafa kamfanin Atlantic International Refinery and Petrochemical.
Ya ce an sa ran cewa matatar zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje da kuma bunkasa tattalin arzikin yankin Neja Delta.

Source: Facebook
Hon. Billy Osawaru ya bayyana cewa an kashe fiye da ₦50bn, amma har yau babu wata alama da ke nuna cewa an fara wannan aiki ballantana batun kammala shi.
Ya bayyana damuwarsa da cewa an taba kai koke ga hukumar EFCC a watan Mayu 2024 kan wannan kudin da aka kashe babu aiki.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato
'Dan majalisa ya magantu kan EFCC
‘Dan majalisar ya bayyana cewa duk da koken da aka kai wa EFCC, har yanzu babu martani daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Ya ce:
“Rashin fara aikin samar da wannan matata ya nuna gaza wa da kuma cin amanar jama’a.”
Shi ma Jagoran ‘Yan adawa a Majalisar, Hon. Kingsley Chinda (PDP, Ribas), ya bayyana takaicinsa kan al’amarin.
Ya bayyana cewa:
“Wannan bangaren mai shi ne ginshikin tattalin arzikinmu, amma mu da kanmu muke janyo wa kanmu koma baya.”
Ya gargadi majalisar kada ta bari wannan kudiri ya zama “kamar kowane” da za a turawa kwamiti ba tare da sakamako ba.
A karshe, majalisar ta umarci kwamitocinta na bangaren man fetur da su binciki wannan lamari cikin makonni hudu, su kuma bayar da cikakken rahoto.
Sun ce binciken zai taimaka wajen gano wadanda ke da hannu, tabbatar da inda kudin ya tafi, da kuma dawo da dukiyar jama’a.

Kara karanta wannan
Atiku: "Gaskiya ta fito da ministan Tinubu ya tona asiri kan kwangilar Legas zuwa Kalaba
Majalisa ta fara bincike kan matatun mai
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta fara bincike kan yadda aka kashe sama da Dala biliyan 18 wajen gyaran matatun mai mallakar gwamnati da ke sassan kasar.
A zaman da ta yi, majalisa ta yi mamakin yadda ake kashe wannan makudan kudi a cikin shekaru 20, amma har yanzu matatun ba su farfado daga dogon suma da su ka yi ba.
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da Hon. Sesi Oluwaseun Whingan ya gabatar a gaban majalisa, inda ya ce lokaci ya yi da za a gano abin da ke hana matatun ci gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng