Bayan Wata 4, Jirgin Shugaban Kasa da Tinubu zai Cefanar Ya Yi Kwantai a Kasuwa
- Jirgin fadar shugaban kasa kirar Boeing 737-700 da aka saka a kasuwa tun watan Yuli, 2025, bai samu mai saye ba har yanzu
- Kamfanin JetHQ na Amurka, wanda ke da alhakin tallata jirgin, ya tabbatar cewa har yanzu jirgin yana nan a kasuwa
- Za a sayar da jirgin ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta fara tsarin rage kashe kudi da kuma rage yawan jiragen shugaban kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jirgin fadar shugaban kasa na Boeing 737-700 da gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa tun watan Yuli, 2025, bai samu mai saye ba har yanzu bayan kusan wata hudu.
Wannan bayani ya fito ne daga kamfanin JetHQ da ke Amurka, wanda ke gudanar da harkar sayar da jiragen sama, ya tabbatar da cewa jirgin “yana nan a kasuwa.”

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Source: UGC
Punch ta wallafa cewa kamfanin ya ki bayar da karin bayani game da taya farashinsa, yana mai cewa irin wannan bayanin sirri ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a samu mai sayen jirgin Najeriya ba
Wata jami'ar kamfanin JetHQ, Marinell Nuevo, ta tabbatar da cewa har yanzu jirgin shugaban kasar bai samu mai saye ba.
Shugabar sashen kasuwancin kamfanin, Laurie Barringer, ta ce ba su da hurumin bayani ga kowa sai ga gwamnatin Najeriya.
The Cable ta rahoto cewa ta bayyana cewa:
“Abin da za mu iya fada kawai shi ne, jirgin har yanzu yana nan a kasuwa.”
An sake tuntubar kamfanin domin neman karin bayani kan dalilin jinkirin sayar da jirgin, amma har zuwa lokacin buga labarin ba a samu amsa ba.
Jirgin ya sha gyara kafin sa shi a kasuwa
Rahotanni sun nuna cewa jirgin yana karkashin kulawar kamfanin AMAC Aerospace da ke kasar Switzerland, wanda ke kula da gyare-gyaren jirage.
A cewar bayanai, an yi wa jirgin manyan gyare-gyare a Basel, Switzerland, a watan Yuli 2024, ciki har da sabunta kujeru, sauya shimfidar cikin jirgin da kuma yi wa injinsa gyara.

Source: UGC
Jirgin yana da kujera 33 ga fasinjoji da ma’aikata takwas, wanda ke nuna cewa yana iya daukar mutum 41 a dunkule.
Farashin jirgin da kudin kula da shi
Shafin aircraftcostcalculator.com ya bayyana cewa farashin matsakaicin jirgi kirar Boeing 737 BBJ da aka taba amfani da shi yana kaiwa Dalar Amurka miliyan 56.
Sai dai shafin ya bayyana cewa farashin na da alaka da shekarar kera shi da irin gyare-gyaren da aka yi masa.
Shafin ya ce jimillar kudin kula da irin jirgin a shekara na kaiwa sama da Dala miliyan 5.2, idan aka hada da man jirgi, kula da inji, da albashin ma’aikata.
An saye jirgin tun lokacin Obasanjo
An saye jirgi ne a shekarar 2005 karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a kan Dala miliyan 43.
Tunda aka saye shi, jirgin na cikin jerin jiragen fadar shugaban kasa, sai dai a watan Yulin 2025 ne gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yanke shawarar sayar da shi.
Legit ta rahoto cewa an yanke shawarin sayar da jirgin ne a wani yunkuri na rage yawan kashe kudin gwamnati.
An bude cibiyoyin samar da aiki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin kafa cibiyoyin samar wa matasa aikin yi.
Bayanai sun nuna cewa cibiyoyin za su hada matasa masu kwarewar aiki da masu bukatar a musu aikin yau da kullum.
Karamar ministar kwadago ce ta tabbatar da kaddamar da shirin a wani taro da aka yi a jihar Legas a ranar Laraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

