Atiku: "Gaskiya Ta Fito da Ministan Tinubu Ya Tona Asiri kan Kwangilar Legas zuwa Kalaba

Atiku: "Gaskiya Ta Fito da Ministan Tinubu Ya Tona Asiri kan Kwangilar Legas zuwa Kalaba

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce Ministan ayyuka, David Umahi ta tabbatar da gaskiyarsa a kan titin Legas-Kalaba
  • A wata hira da aka yi da David Umahi, ya tabbatar da cewa an bayar da kwangilar kowace kilomita na aikin titin a kan N8bn
  • Atiku, wanda ya ce dama ya bayyana haka a baya, ya zargi gwamnati da rashin gaskiya da kuma ɓoye bayanai game da aikin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce Ministan Ayyuka, David Umahi, ya tabbatar da kalamansa a kan aikin ginin tititn Legas zuwa Kalaba.

David Umahi, wanda ya yi wata hira a kwanan nan ya tabbatar da cewa ana aikin, kuma idan aka lissafa ana gina kowace kilomita a kan ₦8bn — adadin da Atiku ya taɓa bayyana wa a baya.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Atiku ya ce agaskiya ta fito
Atiku Abubakar, David Umahi, Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: @omonlakiki
Source: Twitter

A wata sanarwa da hadimin Atiku Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da yaudarar ‘yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu

Tsohon 'dan takarar Shugaban Kasa a jam'iyyar PDP, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da boye gaskiyar ainihin farashi da tsarin biyan kuɗin aikin titin Legas-Kalaba.

Hadimin Atiku, Paul Ibe ya wallafa cewa:

“Lokacin da gwamnatin Tinubu ta sanar da aikin titin gabar teku, Atiku Abubakar ya yi gargadi cewa an yi aringizon farashin aikin zuwa N8bn a kowanne kilomita."
“A wancan lokacin, Ministan Ayyuka ya musanta hakan yana cewa N4bn ne kowane kilomita. Amma yanzu ya amince cewa farashin na kusa da N8bn — dai-dai da abin da Atiku ya faɗa tun farko.”

Sanarwar ta bayyana wannan sabon matsayi na minista a matsayin hujjar rashin gaskiya da boye bayani game da ɗaya daga cikin mafi tsadar ayyukan gine-gine a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya na daukar nauyin Boko Haram? Omokri ya ba sanatan Amurka amsa

Tun da farko, Atiku ya soki tsarin kuɗin aikin da kuma yadda za a biya shi, yana mai cewa akwai shakku a yadda aka dauko biyan kudin kwangiar, kuma wasu 'yan tsiraru ne za su amfana.

Atiku ya nemi bayanan kwangilar Legas-Kalaba

A cewar sanarwar, bayanin da Umahi ya yi na cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da 15% zuwa 30% na kuɗin, yayin da sauran za su fito daga kamfanin mai kwangila, abin tambaya ne.

Atiku ya ce gaskiya ta fito a kan farashin aikin titin Legas-Kalaba
Hoton tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Sanarwar ta ce:

“Waɗanne kamfanoni ne ke bayar da kuɗin? Ta yaya aikin da aka ce mai arha ne ya tashi zuwa adadin da Atiku ya faɗa?”

Atiku ta kuma nemi gwamnatin Tinubu ta fitar da cikakken bayanin kwangilar, daga ciki har da yadda ake biyan kuɗin da abin da gwamnati ke biya daga aljihunta.

Sanarwar ta ce:

“Sau da yawa, Atiku ya nuna kansa a matsayin jagoran ƙasa mai gaskiya wanda ke faɗin abin da yake gaskiya saboda kishin ƙasa, ba siyasa ba."
“Duk wata kwangila da aka cika farashinta, satar dukiyar jama’a ce.”

Shugaban kasa Tinubu ya fusata Atiku

A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa akan yafiyar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu daga cikin mutane 175.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Atiku ya ce matakin bada afuwar ba wai don nuna jinƙai ba ne kawai, har ma da kokarin kawo gyara a shari'ar da ake ganin an tauye wadanda aka daure a lokacin da kotu ta zauna.

Ya ce amma yadda Shugaba Tinubu ya yafe wa mutanen da aka tabbatar sun aikata manyan laifuffuka da su ka hada da safarar miyagun kwayoyi da 'yan ta'adda, abin damuwa ne.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng