Gwamnatin Najeriya na Daukar Nauyin Boko Haram? Omokri Ya ba Sanatan Amurka Amsa
- Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Fasto Reno Omokri, ya karyata zargin cewa gwamnati na daukar nauyin Boko Haram
- Omokri ya kalubalanci wani sanatan Amurka, yana mai cewa ya kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin idan yana da gaskiya
- Wani shugaban gari a Amurka ya goyi bayan Omokri, inda ya yarda gwamnatin Najeriya ba ta da hannu a ayyukan Boko Haram
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Reno Omokri, ya karyata zargin cewa gwamnatin Najeriya na daukar nauyin Boko Haram.
A cewar Mista Reno Omokri, wannan ikirarin da ake yadawa “karya ne, rashin adalci ne kuma babu wata hujja mai karfi da ke goyon bayansa.”

Source: Facebook
Boko Haram: Reno Omokri ya kira taron 'yan jarida
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, tsohon hadimin shugaban kasar, Reno Omokri ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Abuja a ranar Talata.
Reno Omokri ya samu rakiyar Mike Arnold, magajin garin Blanco na jihar Texas da ke Amurka, da kuma Farfesa Khalid Aliyu, sakataren Jama’at Nasril Islam (JNI).
Taron ya biyo bayan maganganun da Sanata Ted Cruz daga Amurka ya yi, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da hannu a ayyukan Boko Haram kai tsaye.
Reno Omokri ya kalubalanci sanatan Amurka
Amma Omokri ya ce:
“Idan Sanata Cruz yana da wata hujja, to ya fadi sunan jami’an gwamnati da ke da hannu a ayyukan Boko Haram.”
Ya kara da cewa:
“Babu wani kisan kare dangi da gwamnati ke yi a Najeriya. Idan akwai jami’an gwamnati da ke taimaka wa ta’addanci, a fadi sunayensu.”
Omokri ya bayyana cewa irin wadannan maganganu na cutar da martabar Najeriya da kuma kokarin da ake yi wajen yaki da ta’addanci.

Source: Twitter
Omokri ya soki manufofin Barrack Obama
A cewar Omokri, manufofin gwamnatin Barrack Obama ne suka taimaka wajen kara karfin Boko Haram a lokacin da rikicin ya fara tsananta.

Kara karanta wannan
Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa
Jaridar This Day ta rahoto Omokri yana cewa:
“A lokacin gwamnatin Obama, manufofinsu sun jefa Najeriya cikin matsalar tsaro. Amma yanzu ana kokarin gyarawa ta hanyar shirye-shiryen tsaro.”
Magajin garin Blanco, Mike Arnold, ya goyi bayan maganar Omokri, yana mai cewa Boko Haram na aikata ta’addanci da kisan gilla, amma ba gwamnatin Najeriya ke daukar nauyinsu ba.
"Idan ana maganar kisan kare dangi, to ba lallai sai da sa hannun gwamnatin Najeriya ba."
- Mike Arnold.
Shi ma Arnold ya ce tsare-tsaren gwamnatin Obama sun taka muhimmiyar raya wajen karfafa ayyukan Boko Haram, ba wai gwamnatin Najeriya ba.
Kisan kare dangi: Majalisar tarayya ta kafa kwamiti
A wani labarin, mu ruwaito cewa, dajalisar dattawa ta kafa kwamitin mutane 12 don nazari kan zargin kisan kiyashi da ake zargin ana yi wa Kiristoci a Najeriya.
Majalisar dattawa ta ce kamitin zai tattara bayanai, ya nemi hujjoji, sannan ya tuntubi majalisar Amurka da ta yi zargin don warware rudanin da aka samu.
Sannan majalisar ta ce za a tura wata tawaga daga kasar nan zuwa Amurka domin bayyana matsayin Najeriya kan zargin da ake yi na kisan Kiristoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

