Mai Gidan Marayu Ya Gamu da Fushin Kotu bayan Kama Shi da Yaran Kano 8 da aka Sace

Mai Gidan Marayu Ya Gamu da Fushin Kotu bayan Kama Shi da Yaran Kano 8 da aka Sace

  • Kotu a Kano ta bayar da umarnin a tura mai gidan marayu zuwa kurkuku bisa zargin satar yara da safarar su zuwa Delta
  • Ana tuhumar mutum uku da laifuffukan hadin baki da satar yara tsakanin shekarar 2016 zuwa 2021 daga jihar
  • Alkalin kotun Amina Adamu-Aliyu ta umurci hukumar NAPTIP da ta gabatar da sauran wadanda ake zargi a zama na gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin a tura Ogugua Christopher, wanda ke da gidan marayu a Asaba, jihar Delta, zuwa gidan yari.

Hukumar NAPTIP da jami'an tsaro sun samu nasarar cafke Ogugua da wasu daga cikin yaran jihar da ya yi safararsu zuwa gidan marayunsa a Delta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta jawo kamfanin kasar China domin taya ta yaki da Lakurawa

Kotu ta aika wanda ake zargi da sace yara zuwa kurkuku
Taswirar jihar Kano da ake zargin barayin yara na cin karensu ba babbaka Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Ogugua na fuskantar shari’a tare da wasu mata biyu — Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta zauna kan sace yaran Kano

Jaridar Leadership ta wallafa cewa ana bisa tuhumar mutanen uku da hadin baki da satar yara guda 15 daga jihar Kano.

Wannan laifi ya saba wa sashe na 97 da 273 na dokar hukunta laifuffuka ta jihar Kano, da kuma sashe na 32(5) na dokar kula da yara da matasa.

Lauyan gwamnati, Barista Salisu Muhammad-Tahir, ya shaidawa kotu cewa wadanda ake zargi sun sace yara da dama tsakanin watan Yuni 2016 da Disamba 2021.

Ana zarginsu da safarar yaran daga jihar Kano zuwa Delta, inda daga nan ne ake sayar da su zuwa wurare daban-daban.

Alƙalin kotu ta ƙi amincewa da buƙatar lauya

A zaman kotun na ranar Talata, Barista Muhammad Tahir ya ce biyu daga cikin wadanda ake tuhuma — Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne — ba su halarci zaman ba, duk da kokarin da aka yi na tabbatar da zuwansu.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya dura China, ya gana da kamfanoni domin kawo cigaba Kano

Ya ce:

"Mun yi iya ƙoƙarinmu don ganin sun halarta, kuma muna ba kotu haƙuri."

Muhammad Tahir ya roƙi kotun da ta dage shari’ar tare da ba da umarnin a ci gaba da tsare Ogugua har zuwa lokacin da za a kawo sauran.

Ana neman mutanen da ake zargi da hannu a sace yaran Kano
Hoton Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Sai dai lauya mai kare wanda ake tuhuma, Gideon Uzo, ya roƙi kotu da ta bar Ogugua a hannun hukumar hana safarar mutane (NAPTIP) maimakon a tura shi gidan gyaran hali.

Amma Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta ƙi amincewa da bukatar, tare da bayar da umarnin a tsare Ogugua a gidan gyaran hali.

Haka kuma ta umarci hukumar NAPTIP da ta tabbatar da kawo sauran wadanda ake zargi a zaman kotun na gaba, wanda aka dage zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2025.

Fatan iyayen yara a Kano

Kwamred Isma'il Ibrahim Muhammad, shi ne Shugaban ƙungiyar iyayen da aka sace wa yaransu a Kano, ya shaida wa Legit cewa dama sun gayyaci sauran iyaye su halarci zaman kotun.

Kara karanta wannan

Ta tashi: Ganduje da ƴaƴansa sun shiga uku, gwamnatin Kano ta maka su a kotu

Ya ce:

"Mun dade muna bibiyar yaran, lokacin da mu ka je Asaba, mun samu yara da dama, mun gano wadanda aka sace daga Kano guda takwas."

Ya kara da cewa suna fatan za a yi masu adalci, tare da kira ga sauran iyaye da su ci gaba da addu'a da sa ido a kan yaransu.

Kotu ta hukunta barayin yaran Kano

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Jihar Kano ta hukunta Paul Owne, wanda ake zargin ya jagoranci masu satar yara daga jihar Kano zuwa jihohin da ke Kudancin kasar nan.

An gurfanar da Paul ne bisa laifuka 38 da ake zarginsa tare da wasu mutane shida, suna satar yara ƙasa da shekaru 10, lamarin da ya sa kotun ta yi masa hukuncin daurin shekaru 104.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf, wadda ta jagoranci shari’ar, ta rarraba laifukan zuwa rukuni uku, a kowane laifi daga cikin rukuni biyu, an yanke masa hukuncin shekaru bakwai.

Kara karanta wannan

Tauraruwar Kano ta kara haskawa, jihar ta samu babban nasara a sauyin yanayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng