An Yanke Wa Jagoran Waɗanda Ke Sace Yaran Kano Su Sayar Da Su a Kudu Ɗaurin Shekaru 104 Tare Da Tarar Kuɗi

An Yanke Wa Jagoran Waɗanda Ke Sace Yaran Kano Su Sayar Da Su a Kudu Ɗaurin Shekaru 104 Tare Da Tarar Kuɗi

  • Kotun jihar Kano ta yanke wa jagoran masu satar yara daga Kano suna sayarwa a kudu daurin shekara 102
  • Bayan daurin na shekaru 102, kotun ta kuma ci Mr Paul Owne tarar kudi Naira 100,000 bayan ya amsa laifukansa
  • Sauran mutane biyar da ake zargin suna aiki tare da Paul Owne sun musunta tuhumar da ake musu don haka za a saka ranar shari'arsu

Kano, Kano - Babban kotun jihar Kano ta yanke wa Paul Owne, jagoran wadanda ke sace yaran Kano da sayar da su jihohin kudu hukuncin daurin shekaru 104 a gidan gyaran hali, Daily Trust ta ruwaito.

Kotun, wadda Mai shari'a Zuwaira Yusuf ke jagoranta ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifuka 38 da gwamnatin jihar ke zarginsa da aikatawa.

An Yankewa Jagoran Waɗanda Ke Sace Yaran Kano Su Sayar Da Su a Kudu Ɗaurin Shekaru 104 Tare Da Tarar Kuɗi
An yankewa jagorar barayin yaran Kano daurin shekaru 104. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar rahoton na Daily Trust, an gurfanar da shi ne bisa hada baki da wasu mutane shida domin sace wasu yara masu shekaru kasa da 10 a Kano kuma suka sayar da su a Onitsha, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Sauran mutane biyar din da ake zargi da hadin baki wurin aikata laifin, Ogbono, Emanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha da Chinelo Ifedigwe, ba su amsa laifin ba don haka za a fara sauraron kararsu.

Yadda alkali ta yanke wa Paul hukuncin daurin

Da ta yanke hukuncin a ranar Juma'a, Mai Shari'a Yusuf ta kasa laifukan zuwa gida uku.

Kashi na farko, kotun ta tabbatar cewa an samu wanda aka yankewa hukuncin da aikata laifuka na 2, 8, 9, 2, 27 da 34, don haka, ta yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a kowannensu ba tare da zabin biyan tara ba sannan da tarar N100,000.

Kazalika, kotun ta same shi da rashin gaskiya a kan laifuka na 3, 5, 10, 11, 22, 28 da 38 kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai.

A rukunin na karshe, Mai Shari'a Yusuf ta ce abin da Paul ya aikata ya saba doka a laifuka na 4, 12, 13, 29 da 38, saboda haka aka yanke masa hukuncin daurin shekara hudu a kowannensu ba tare da zabin biyan tara ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

Ta bada umurnin cewa za a gwamutsa masa hukuncin daurin ne su tafi a tare.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel