Sojoji Sun Kama Miji da Mata Masu Safarar Makamai ga Ƴan Ya'adda a Jihohin Arewa
- Sojoji sun cafke wasu ma'aurata da ake zargi suna safarar makamai ga ‘yan ta’adda a jihohin Arewa maso Yamma
- An kama Abdullahi Balarabe da matarsa Shafaatu, kuma an gano harsasai 1,207 da ake shirin kaiwa ga ‘yan ta’adda
- Kwamandan JTF-OEP ya ba jihohin Arewa tabbaci na ƙara ƙaimin dakarun hadin gwiwa wajen yaki da ƴan ta’adda
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna – Rundunar tsaro ta hadin gwiwa (JTF-OEP) ta samu nasarar kama wani miji da matarsa da ake zargi da safarar makamai.
An rahoto cewa miji da matar sun kware a sayar da makamai ga kungiyoyin ƴan tadda a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Source: Twitter
An cafke miji da mata kan safarar makamai
Jaridar Punch ta rahoto cewa, an bayyana sunan wadanda aka kama da Abdullahi Balarabe, mai shekaru 40, da matarsa Shafaatu Abdullahi mai shekaru 18.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya kuma nuna cewa an cafke su ne a wani shingen bincike na bazata da aka kafa a Saminaka, karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, Major Samson Zhakom, ne ya tabbatar da wannan kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata.
Wani bangare na sanarwar ta ce:
"Sojojin hadin guiwa sun bi diddigin wasu manyan masu safarar makamai biyu kuma suka kama su a ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025.
“An cafke wadanda ake zargi, Mista Abdullahi Balarabe (40) da matarsa, Shafaatu Abdullahi (18), a wani wurin bincike na gaggawa da ke jihar Kaduna.”
Sojoji sun kama harsasai 1,207 a Kaduna
A cewarsa, binciken bayanan sirri daga wata hukuma a jihar Filato ne ya kai ga gano ma’auratan masu safarar makamai.
Yayin bincike, sojojin sun gano harsasai 1,207 kirar 7.62mm da ake zargin ma'auratan za su kai su ga kungiyoyin ta’addanci da ke addabar Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama
“An kama su ne a karkashin hadin gwiwar rundunonin Operation ENDURING PEACE da Operation FANSAN YAMMA a wajen garin Saminaka.
“Dukkan kayayyakin da aka samu yanzu suna hannunmu domin gudanar da cikakken bincike da kai samame kan sauran wadanda ke da hannu cikin wannan harkar.”

Source: Twitter
An yaba da kokarin sojojin hadin gwiwa
Sanarwar ta kuma ruwaito GOC na runduna ta uku (3), kuma kwamandan JTF-OEP, Manjo Janar Folusho Oyinlola, yana yaba wa jarumtar sojojin da jajircewarsu.
Shafin Zagazola Makama ya rahoto Manjo Oyinlola ya na cewa:
“Wannan nasara ta nuna mahimmancin hadin gwiwar hukumomin tsaro wajen magance laifuka da ta’addanci.”
Oyinlola ya tabbatar wa mazauna jihohin Filato, Kaduna da makwabtansu cewa rundunar za ta ci gaba da kafa matakan tsaro masu karfi don dawo da zaman lafiya.
“Ba za mu gaji ba wajen murkushe ayyukan ‘yan ta’adda da masu laifi, domin tabbatar da an samu zaman lafiya a Arewa maso Yamma."
- Janar Folusho Oyinlola.
An gano gidan da ake boye makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun cafke wasu mutane a jihar Taraba da ake zargin suna hada kai da yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar soji a jihar Taraba, Kyaftin Oni Olubo ya tabbatar da cafke mutanen da ake zargin a ƙaramar hukumar Lau.
Kyaftin Oni Olubo ya bayyana rawar da yan Najeriya za su iya takawa wajen taimakawa jami'an tsaron kasar nan don magance matsalar tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

