Edo: Gwamna Ya Ɗauki Mataki mai Tsauri, Ya Kori Kwamishina daga Aiki
- Gwamna Monday Okpebholo ya kori Samson Osagie daga matsayin kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati
- Rahotanni sun nuna cewa sauke Osagie na da alaƙa da sake fasalin ma’aikatu da ƙara yawansu zuwa guda 28 a jihar Edo
- An dade ana hasashen cewa kwamishina zai rasa mukaminsa, tun bayan da aka saki sunayen sababbin kwamishinonin jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo – Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sauke Hon. Samson Osagie daga mukaminsa na kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Edo.
Babu wani dalili da aka bayyana a hukumance game da korar Osagie, wanda ya kasance ɗaya daga cikin kwamishinoni na farko da aka rantsar lokacin da Okpebholo ya karɓi mulki.

Source: Twitter
An dade da hango korar kwamishinan
Rahoton The Nation ya nuna cewa, an dade ana hasashen cewa Osagie zai rasa mukaminsa, tun bayan da aka bayyana sunayen sababbin kwamishinoni, ciki har da Farfesa Roland Otaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko da yake ba a bayyana korar tasa a fili ba, amma ba a ga sunansa a cikin jerin sababbin kwamishinoni da gwamna ya nada ba.
Bayan wannan sauyi, Gwamna Okpebholo ya ƙara adadin ma’aikatun gwamnatin Edo zuwa guda 28, a wani yunƙuri na ƙara daidaito da inganci a gudanar da mulki.
Kwatsam, sai kuma ga shi yau Talata, 14 ga watan Oktoba, 2025, gwamnatin jihar ta sanar da korar kwamishinan daga aiki, ba tare da fadin dalili ba.
Gwamna ya nada sababbin kwamishinoni
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin Edo, Musa Ikhilor, ya fitar, gwamnati ta ce ƙarin ma’aikatun zai taimaka wajen daidaita manufar SHINE na gwamnan da Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tsarin zai inganta aikin gwamnati, haɗin kai a sassan ayyuka, da kuma ƙarfafa isar da shirye-shirye ga al’umma.
A cikin sabon tsarin, ba a naɗa kwamishina a ma’aikatar fasaha, al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire ba.
Sr. Felix Ehiguese Akhabue zai jagoranci ma’aikatar ayyuka, yayin da Hon. Andrew Ijegbai ya zama kwamishinan ma’adinai.
Prince Kassim Afegbua ya karɓi ma’aikatar sadarwa da tsare-tsare, inda Paul Ohonbamu ya koma ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da masarautu.

Source: Facebook
Kwamishinan da aka kora ya yi martani
Dr. Jerry Uwangue ya zama kwamishinan noma da tsaron abinci, yayin da Farfesa Omorodion Ikponwosa zai jagoranci ma’aikatar kiwo.
Haka kuma, Barr. Nosa Adams ya karɓi ma’aikatar muhalli, Dr. Paddy Iyamu da Dr. Cyril Oshiomhole sun ci gaba da jagorantar ilimi da lafiya.
A martaninsa, Samson Osagie ya bayyana cewa ya gamsu da damar da Gwamna Okpebholo ya ba shi, yana mai cewa gwamnan ya yi abin da ya dace ne.
“Na gode da damar da aka ba ni na yi wa jihata aiki. Gwamna Okpebholo ya yi abin a yaba."
- Hon. Samson Osagie.
Gwamna ya kori kwamishinan shari'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya sallami Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar daga aiki.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu
An tabbatar da sallamar kwamishinan ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da dabaru na jihar Imo, Cif Declan Emelumba ya fitar.
Sai dai, an tattaro cewa sanarwar ba ta yi bayani game da dalilin da ya sa mai girma gwamna ya tsige Barista Akaolisa daga mukaminsa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

