Maryam Sanda: Mahaifin Marigayi Bilyaminu Ya Yi Magana bayan Afuwar Tinubu
- Mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa ya yi magana bayan afuwar shugaban kasa Bola Tinubu
- Dattijon ya ce ya amince da afuwar da Shugaba Tinubu ya yi ga Maryam Sanda, yana mai cewa ya dade da yafewa
- Ya ce fansa ba za ta dawo da ɗansa ba, amma yafiya tana kawo zaman lafiya, yana mai kira da a bar komai ga Allah SWT
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya magantu bayan afuwa da Bola Tinubu ya yi ga matar ɗansa.
Dattijon ya bayyana cewa ya amince da afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga surukarsa, Maryam Sanda, wanda aka daure bisa laifin kashe mijinta.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu

Source: UGC
Hakan na cikin faifan bidiyo da Punch ta yada wanda Legit Hausa ta bibiya a yau Talata 14 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin da aka yankewa Maryam Sanda
An yankewa Maryam Sanda, ’yar tsohon jami’in Aso Savings hukuncin kisa ta hanyar rataya a watan Janairu 2020.
Hakan ya biyo bayan tuhumarta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a rikicin da ya barke tsakaninsu a cikin gida Abuja a shekarar 2017.
Wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a a wancan lokaci inda aka yi ta kiran hukumomi su dauki matakin da ya dace da ita.
Maryam Sanda: Mahaifin Bilyaminu ya yi magana
Dattijon ya ce tuni ya yafe mata tun kafin hukuncin kotu, yana mai bayyana afuwar a matsayin nufin Allah.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, tsohon Alhajin ya ce yana farin ciki da cewa “uban ƙasa” ya saki Maryam domin ta kula da ’ya’yanta biyu.

Kara karanta wannan
Hon. Farouk Lawan ya tabo batun rayuwa a gidan yari bayan Tinubu ya yi masa afuwa
Ya ce:
“Mun yarda da duk abin da Allah ya kawo garemu. Na yafe mata, ba ni da wata ƙiyayya ga gwamnati ko danginta.”

Source: Facebook
Mahaifin Bilyaminu ya fadi muhimmancin yafiya
Alhaji Bello ya bayyana cewa tun kafin kotu ta yanke hukunci, ya riga ya rubuta wasiku da dama ga hukumomi, ciki har da tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN, yana roƙon a tausaya mata.
Ya tabbatar da cewa afuwa na kawo zaman lafiya fiye da daukar fansa ko kuma biyan diyya.
A ranar Litinin, wani ɓangare na dangin marigayin ya soki afuwar, suna kiran hakan rashin adalci amma Alhaji Bello ya ce hakan ba ra’ayinsa ba ne. Ya bayyana cewa:
“Ni uban marigayin ne, na zabi yafiya domin zaman lafiya, domin ’ya’yanta da kuma rahamar Allah.”
Dangi sun ji haushin yafewa Maryam Sanda
Mun ba ku labarin cewa yan uwan marigayi Bilyaminu Bello sun soki yafiyar da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, wadda aka tabbatar ta kashe mijinta.

Kara karanta wannan
'Yan uwan Bilyaminu sun shiga kunci, sun yi tir da Tinubu ya yafe wa Maryam Sanda
Sun ce wannan mataki na gwamnatin Tinubu ta dauka babban rashin adalci ne da ya sake bude masu zafin kisan 'dan uwansu da Maryam ta yi.
Iyalin sun bayyana cewa Maryam ba ta taɓa nuna nadama ba tun bayan kisan, wannan yafiya da Bola Tinubu ya yi ta kara jefa su a cikin wani hali.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng