Hukuncin kisa: Muhimman abubuwa a kan alkalin da ya yanke wa Maryam Sanda hukunci

Hukuncin kisa: Muhimman abubuwa a kan alkalin da ya yanke wa Maryam Sanda hukunci

Mai shari'a Yusuf Halliru a ranar Litinin ya yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan kisan mijinta Bilyaminu Bello da tayi. Wannan kuwa ba bakon alkali bane.

Jastis Halilu ne ya yankewa Ibrahim Garba Wala, wanda aka fi sani da IG Wala, hukuncin daurin shekaru 7 a gidan gyaran hali a kan bata sunan shugaban hukumar Hajji ta kasa.

Hakazalika, a watan Nuwamba 2017, Jastis Halilu ya yankewa wasu daraktoci biyu shekaru 35 a gidan Yari. Daratoci Abdullahi Dogonyaro da Yahaya Ayodeji na karkashin ofishin babban akawun kasa ne Mohammed Dogon Audu a wancan lokacin.

A lokuta da yawa, alkalin ya caccaki rundunar sojin Najeriya, 'yan sanda da EFCC a kan yadda suke amfani da kujerarsu ba ta yadda ya dace ba.

A watan Mayu na 2016, Halilu ya caccaki EFCC da sojin Najeriya na yadda suka garkame tsohon mai bada shawara kan tsaro, Sambo Dasuki ba tare da sun bada belinsa ba. "EFCC kirkirar shari'a ce. Kotu ba za ta barta tana aiki kamar ta fi karfin shari'a ba duk da kuwa taken su na nuna babu wanda yafi karfin shari'a.

DUBA WANNAN: Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

"EFCC ba ta fi karfin kundin tsarin mulkin kasar nan ba. Masu gabatar da kara na aiki kamar ba a karnin wayewa suke ba. Suna aiki kamar a zamanin mulkin soji inda ake kama mutum kuma a sake shi a lokacin da aka so. Ina da kwarin guiwar cewa EFCC da sojin Najeriya na yi kamar jahilai," cewar alkalin.

An haifa Jastis Halilu a ranar 15 ga watan Augusta, 1972 a karamar hukumar Nasarawa Eggon da ke jihar Nasarawa. Ya samu digirinsa na farko a jami'ar Jos a fannin lauyanci a 1997. Ya je makarantar horar da lauyoyi a 1998 kuma an rantsar da shi a wannan shekarar.

Ya yi digirinsa na biyu a fannin lauyanci a jami'ar Jos din a 2001. Bayan shekarun da ya dauka yana aikin kashin kanshi, Halilu ya samu aiki a matsayin alkali a babbar kotun tarayya a watan Yuni na 2010. Yana da aure da kuma 'ya'ya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel