Batanci: Sheikh Lawal Triumph Ya Fitar da Bayanai bayan Zama da Shura a Kano
- Sheikh Lawan Abubakar Shua’ibu Triumph ya bayyana sakamakon ganawarsa da Shura a Kano bayan zarge-zargen da aka yi masa
- Malamin addinin ya bayyana cewa an gabatar masa da tambayoyi masu zurfi sosai, inda ya gabatar da hujjoji daga littattafan da suka dace
- Shura ta shawarce shi ya tausasa harshe a lokacin wa’azi, kuma ya bayyana matakin da zai dauka game shawarin da aka ba shi a zaman
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Bayan ganawa da Shura da ya yi a ranar 13, Oktoba, 2025, malamin addinin musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Shua’ibu Triumph ya yi karin haske.
Malamin ya yi karin haske ne kan abubuwan da suka tattauna a zaman da suka yi da malamai da dattawan jihar Kano.

Source: Facebook
A wani bidiyo da shafin Musaha TV ya wallafa a Facebook, malamin ya ce an gayyace shi domin ya bayyana matsayinsa kan wasu zarge-zarge da aka yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bayaninsa, Sheikh Triumph ya ce ya gabatar da hujjoji da misalai daga littattafan ilimi, kuma Shura ta saurare shi cikin nutsuwa tare da ba shi shawarwari.
Shawarin Majalisar shura ga Sheikh Triumph
Sheikh Triumph ya bayyana cewa Shura ta nuna gamsuwa da bayanan da ya gabatar, sai dai ta ba shi shawarar ya tausasa harshe a lokacin da yake wa’azi.
Ya ce sun bukaci ya rika kula da lafazin da yake amfani da shi domin kada ya haifar da rudani ko rikici tsakanin mabiya.
A cewarsa, ya amince da wannan shawara a matsayin dalibin ilimi, domin a cewarsa, malaman sun riga shi fara wa'azi kuma za su iya hango abin da bai hango ba.
Sheikh Triumph ya ba da hakuri?
Game da batun cewa ya bayar da hakuri, Sheikh Triumph ya ce bai aikata wani abu da zai bukaci afuwa ba, amma ya bayyana cewa ya yafe wa duk wanda ya zage shi bisa rashin fahimta.
Ya ce wasu mutane sun karkatar da kalamansa, suna amfani da su wajen yada abin da bai fada ba, a kan haka ya ce wasu suka rika zaginsa.

Source: Facebook
Kiran Lawal Triumph ga al’ummar Kano
A karshen bayanin da ya yi, Sheikh Lawan Triumph ya yi kira ga jama’an Kano da su rungumi koyarwar sunnah da ilimi mai tsafta wajen magance matsalolin addini.
Malamin ya kuma nuna godiya ga malamai da 'yan kwamitin Shura bisa yadda suka saurare shi da mutunci da kuma niyyar inganta fahimtar addini a jihar Kano.
Legit ta tattauna da Hamza Abdullahi
Yayin zatawa da Legit Hausa, Ustaz Hamza Abdullahi ya ce zaman bai kasance kamar yadda ya ke tsammani ba.
Ya bayyana cewa:
"Na yi tsammani za su tattauna da shi ne kawai su dauki bayanai ba tare da alamar jayayya ba."
"A abin da ya faru, akwai alamar su kan su 'yan kwamitin kansu ba a hade ya ke ba."
Malaman da aka zarga da batanci
A wani rahoton, kun ji cewa bayan Sheikh Lawan Triumph, an zargi wasu malaman addinin Musulunci da batanci a Najeriya.
Cikin malaman da aka zarga akwai marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dusten Tanshi a Bauchi, sai dai ba a yi zama da shi kan zargin ba.
A jihar Kano kuma, an zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda aka zauna da shi domin ya yi bayani kan abin da ya fada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


