Bayan Rikicin Dangote da PENGASSAN, Kamfanin NNPCL Ya Yi Kari kan Farashin Litar Fetur
- Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya yi kari kan farashin da yake sayar da litar fetur a gidajen man da ke mallakinsa
- NNPCL ya yi karin farashin litar fetur din ne a Legas da babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025
- Sabon farashin ya nuna cewa an samu karin N127 a Legas sabanin yadda ake sayar da fetur na N865 kan kowace lita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya kara farashin fetur zuwa N992 kan kowace lita a birnin Legas.
Hakazalika, kamfanin na NNPCL ya kara farashin litar fetur zuwa N955 a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Getty Images
Meyasa NNPCL ya kara farashin litar fetur
Jaridar TheCable ta lura cewa sabon farashin ya fara aiki a yawancin tashoshin sayar da mai na NNPCL da ke cikin waɗannan birane a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025.
Har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto, babu wata sanarwa ta hukuma daga kamfanin NNPCL da ta bayyana dalilin karin farashin na fetur.
A yawancin gidajen man NNPCL da jaridar The Nation ta ziyarta, an hango ma’aikata suna daidaita injinan famfo don nuna sabon farashin.
A gidan man kamfanin NNPCL da ke kan titin Ogunusi, Ojodu Berger a jihar Legas, ma’aikatan sun bayyana cewa an ba su umarnin su canza farashin zuwa N992 kan kowace lita.
Sabon farashin ya nuna karin N127 a Legas, daga tsohon farashin N865 kan kowace lita, da kuma karin N65 a Abuja, daga N890 kan kowace lita.
A gidan man NNPCL da ke Ago Palace Way, Legas, an tabbatar da cewa farashin fetur ya tashi zuwa N992 kan kowace lita.
Sai dai binciken da aka gudanar a yankin Ibafo da ke kan titin Legas–Ibadan, ya nuna cewa gidajen man NNPCL da ke wurin, suna nuna tsohon farashin N875 kan kowace lita, duk da cewa ba sa sayarwa ga masu motoci a lokacin.

Kara karanta wannan
Amupitan: Lauyoyi na shirin kawo cikas ga tabbatar da nadin shugaban INEC a majalisa
Karin farashin fetur ya shafi birnin Abuja
A birnin Abuja kuwa, ana sayar da fetur a N955 kan kowace lita a gidan man kamfanin NNPCL da ke cikin Kubwa.

Source: Facebook
Hakazalika ana sayar fetur din a irin wannan farashin a wani gidan man NNPCL da ke a kan titin Komolafe, Lugbe a cikin babban birnin tarayya Abuja.
Wannan karin farashin ya soke ragin da aka aiwatar a ranar 15 ga watan Agustan 2025, lokacin da NNPCL ya saukar da farashin fetur zuwa N865 a Legas da N890 a birnin Abuja.
Majalisa ta fara binciken kamfanin NNPCL
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta fara yunkurin bincikar kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).
Majalisar wakilan za ta binciki kamfanin na NNPCL ne kan yadda aka kashe Dala biliyan 18 wajen gyaran matatun mai a kasar nan.
Majalisar ta ce an kashe wannan kudi don farfado da matatun mai mallakar gwamnati da ke Port Harcourt, Warri da Kaduna cikin shekaru 20, amma ba labari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
