Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane, Ezigbe Ya Ci Moriyar Afuwar Shugaba Tinubu
- An hango fitinannen 'dan ta'adda da ya kware a garkuwa da mutane, Kelvin Oniarah a cikin mutanen da Bola Tinubu ya yi wa afuwa
- Ezigbe na daga cikin mutanen da Shugaban Kasa Tinubu ya rage wa wa'adin zaman gidan kurkuku daga ɗaurin shekaru 20 zuwa 13
- Kelvin Ezigbe, wanda ya addabi jihar Delta da garkuwa da mutane, ya samu afuwa bisa wadansu canje-canjen hali da gwamnati ta ce ya nuna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Kelvin Oniarah Ezigbe, shahararren mai garkuwa da mutane wanda ya sace Mike Ozekhome (SAN) a shekarar 2013, ya samu rahamar Bola Tinubu.
Shugaban Kasa ya sanyi fitinannen mai garkuwa da muatnen a cikin jerin mutum 175 da ya yi wa afuwa saboda dalilai daban-daban.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi afuwa ga babban soja da aka kama ya sayarwa ƴan ta'adda makamai 7000

Source: Facebook
Sanarwar da hadimin Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook, ta bayyana dalilin da ya sa aka sassauta hukuncin da kotu ta yi wa Oniarah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi wa fitinannen 'dan ta'adda afuwa
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa fitinannen dan ta'adda, Kelvin rangwamen hukunci daga shekaru 20 zuwa shekaru 13.
An bayyana cewa Kelvin Oniarah Ezigbe na cikin mutane 175 da suka samu afuwa ko rangwamen hukunci daga gwamnatin tarayya, bayan amincewar Majalisar Ƙoli ta Ƙasa.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabaru, ya bayyana cewa an rage wa Ezigbe hukuncinsa.
Ya kara da cewa an yi ragin shekarun ne saboda ya nuna nadama da kuma shiga karatu a National Open University of Nigeria (NOUN).
Ya ce:
“An rage masa hukunci daga shekaru 20 zuwa 13 saboda nadama da kuma shiga jami’a da ya yi."
Yadda Ezibge ya fitini mutanen Delta
Kafin a kama shi a watan Satumbar 2013, Ezigbe ya kasance fitaccen mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar Delta, musamman yankin Kokori a karamar hukumar Ethiope East.
A ranar 23 ga Agusta, 2013, Ezigbe da tawagarsa sun sace babban lauyan nan, Mike Ozekhome SAN da direbansa a kan hanyar Benin-Auchi da ke jihar Edo.
A lokacin da ‘yan sanda suka yi ƙoƙarin ceto Ozekhome, Ezigbe da mutanensa sun kashe jami’an ‘yan sanda huɗu a wani kwanton-bauna.

Source: Facebook
A shekarar 2012, an danganta kungiyar Ezigbe da sace Hope Eghagha, tsohon kwamishinan ilimi na jihar Delta, yayin da yake tafiya daga Warri zuwa Asaba tare da kashe dan sanda.
Haka nan, tawagar Ezigbe ta kashe jami’an kurkuku biyu a lokacin da suke jigilar wasu daga cikin 'yan kungiyar.
A watan Yuni 2024, an gurfanar da shi a kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ta’addanci, garkuwa da mutane, da ɗaukar nauyin aikata laifi.
Mike Ozekhome, da ya sace, ya shaida wa kotu cewa an rufe shi tsawon makonni uku, kuma an sako shi ne bayan an biya fansar N40m.
Tinubu yayi afuwa ga mai sayar da makamai
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba da afuwa ga wani babban soja da ake tuhumarsa da siya da siyarwa ‘yan ta’adda makamai kimanin 7,000.
Wannan afuwa wani ɓangare ne na rangwamen laifuffuka ga mutane 175 da gwamnatin tarayya ta amince da shi, lamarin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a kasar nan.
Rahotanni sun nuna cewa wannan soja ya kasance cikin wadanda aka jera a cikin jerin mutane da za a yi wa afuwa, musamman bisa laifukan manya da aka tabbatar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

