Sauya Shekar Gwamnoni, Jagoran APGA Ya Zargi Majalisa da Zama 'Yar Amshin Shata

Sauya Shekar Gwamnoni, Jagoran APGA Ya Zargi Majalisa da Zama 'Yar Amshin Shata

  • Chekwas Okorie ya ce yawancin gwamnoni na tserewa zuwa APC saboda tsoron EFCC bayan karewar wa’adinsu a mulki
  • Ya zargi majalisar tarayya da zama 'yar amshin shata, musamman wajen gaza hana sauya sheka ba bisa ka’ida ba tsakanin jam’iyyu
  • A cewar jigon jam'iyyar ta APGA, 'yan majalisa na da damar wofantar da kujerar duk wanda ya fice daga jam'iyyar da ya ci zabe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Tsohon shugaban jam’iyyar APGA, Chief Chekwas Okorie, ya bayyana dalilin da ya sa yawancin gwamnonin jam’iyyun adawa ke sauya sheka zuwa APC.

Chief Chekwas Okorie ya bayyana cewa gwamnonin adawa na tururuwar komawa APC saboda suna tsoron haduwa da hukumar EFCC bayan karewar wa’adinsu.

Chekwas Okorie, jigon APGA ya ce gwamnonin adawa na tsoron EFCC shi ya sa suke komawa APC
Jagoran jam'iyyar APGA na kasa, Chief Chekwas Okorie, yana jawabi ga manema labarai. Hoto: @chekwas_okorie
Source: Twitter

'Abin da ke sa gwamnoni shiga APC' - Okorie

Kara karanta wannan

APGA: Yadda tsoron EFCC ke kora gwamnoni, 'yan adawa zuwa APC

A wata tattaunawa da jaridar Vanguard, Okorie ya bayyana cewa gwamnoni da dama na ganin shiga APC tamkar mafaka ce daga tuhumar rashawa da za su iya fuskanta daga hukumar EFCC bayan sun sauka daga mulki.

Chief Okorie ya ce yawancin wadannan gwamnoni sun yi amfani da girman mukam ansu wajen aikata laifuka da almundahana.

A cewarsa, sun yi hakan ne saboda sun san sashe na 308 na kundin tsarin mulki ya basu kariya daga gurfanar da su a kotu yayin da suke mulki.

“Suna jin tsoron tozarcin da EFCC za ta musu idan sun rasa kariyar ofis, shi ya sa suke guduwa zuwa jam’iyyar da ke mulki."

- Chief Chekwas Okorie.

Ya kara da cewa, wannan salon da gwamnonin jam'iyyun adawa ke amfani da shi na tserewa zuwa jam’iyya mai mulki bai taba tsare kowa daga tuhuma ba.

Gwamnoni na garari bayan kammala wa'adinsu

Jagoran na jam'iyyar APGA ya tuna yadda wasu daga cikin gwamnonin kasar nan da suka tsaya takarar majalisar dattawa bayan shekara takwas a kan mulki, suka sha kaye a zabe.

Okorie ya bayyana cewa, akalla gwamnoni shida da suka yi mulki tsawon shekaru takwas sun kasa lashe kujerar majalisar dattawa a zaben da ya gabata, inda ɗaya kacal cikin su ya samu mukami daga fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2027: APC ta samu matsala a shirin da ta so yi a jihohin Najeriya 36

Ya soki tsarin siyasar Najeriya, yana mai cewa:

“Ba su da wani tabbacin samun wani mukami. Ire-iren halayensu ne ke lalata tsarin dimokuraɗiyya. Kuma ga majalisar dokoki ta kasa ta gaza cika nauyinta.”
Jagoran APGA, Chekwas Okorie, ya ce gwamnonin adawa na shiga APC don tsira daga binciken EFCC bayan sauka daga mulki
Jami'an hukumar EFCC suna tattaunawa a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: UGC

Jigon APGA ya caccaki 'yan majalisar tarayya

Chief Okorie ya zargi majalisar dokoki ta tarayya da zama “'yan amshin shata” na bangaren zartarwa ta kasa.

Ya ce ya kamata dokar kasa ta tilasta kowane dan siyasa da ya bar jam’iyyarsa rasa kujerarsa kai tsaye, sannan hukumar INEC ta gudanar da sabon zabe.

“Ta haka ne za mu tabbatar da gaskiya. Amma yanzu mutane na cin moriyar jam'iyyar da suka hau kujera su yada korenta, su sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki don kare kawunansu."

- Chief Chekwas Okorie.

Gwamnoni 3 za su koma jam'iyyar APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta samu karin gwamnoni uku da za su baro tsagin adawa zuwa cikinta a makon nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya fadi abin da yake ji kan gwamnonin da ke ficewa daga PDP zuwa APC

Rahotanni sun gano sunayen gwamnoni biyu daga ciki, wadanda za su sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Daga cikin waɗanda ake tsammani za su koma APC akwai Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu da Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, kuma za su koma tare da jama'arsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com